15/09/2026
بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا"
Cikin alhini da juyayi muke miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga Sahibul Asr (Ajjalallah Farajahu Sharif), da jagoran mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
Na Rashin; Marhum Muhammad Abdullahi
Yau Talata: 15/09/2026. Yayi dai dai da kwana uku na rasuwar: Marhum Muhammad Abdullahi
Marhum ya kasance jajirtaccen ɗan uwa mai sallamawa da jajircewa, k*ma hazikin matashi mai himma wajen kula da addini, sannan ya kasance cikakken ma'aikaci a cikin matasa na rundunar Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky (JASAZ) a Zone ɗin Mukhtar Assakafy, k*ma mai bada gudunmawa da himma wajen sauke nauyin da ke kansa.
Ya rasu a ranar Lahadi. 13/09/2026, sak**akon accident da ya ritsa dashi akan hanyar dawowa Muzahara a garin Wurno zuwa Achida wanda anan ya cimma wa'adin sa.
Muna ƙara miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyaye, abokai da ƴan uwansa, Allah ya girmama matsayin sa ya karɓi uzurinsa, ya sadashi da Shahidan Muslumci.
Muna roƙon ƴan uwa da su sanya shi cikin addu'oin su tare da barar Fatiha daya, da Salatin Annabi goma sadaukarwa zuwa ga ruhin sa.
KULLU NA AHMAD YA ABA AHMAD
JASAZ Shuhada Department.
15/09/2026.