MAI AGOGO

MAI AGOGO Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MAI AGOGO, Grocers, Fish Market, Apo Resettlement, Abuja, Abuja.

MASU SAUKI NE❣
03/06/2026

MASU SAUKI NE❣

MAKIRCIN DA AKA ƘULLA A DARREN JIYA KAN JIHAR GOMBE DA TASIRIN PROFESSOR ISA ALI PANTAMI An gudanar da wani taro a Gidan...
03/06/2026

MAKIRCIN DA AKA ƘULLA A DARREN JIYA KAN JIHAR GOMBE DA TASIRIN PROFESSOR ISA ALI PANTAMI

An gudanar da wani taro a Gidan Gwamnati a daren jiya, Talata 2 ga Yuni, 2026. A cewar bayanan da s**a fito daga taron, babban abin da ya mamaye tattaunawar shi ne Malam Isa Ali Pantami, inda aka mayar da hankali kan muhimman batutuwa uku:

1. Sun sani sarai cewa Malam Isa Ali Pantami bai shiga abin da suke ƙira zaɓen fidda gwani ba. Duk da haka, an yi shawarar cewa a ci gaba da tayar da hayaniya a kan lamarin tare da amfani da wasu da ake ƙira masu ruwa da tsaki daga cikin gida domin jawo ruɗani da tsawaita cece-kuce.

2. Karɓuwar da Professor Isa Ali Pantami da sabuwar jam’iyyarsa ta PDP suke samu a faɗin jihar Gombe na ƙara damun su matuƙa. Shigowarsa ya sake farfaɗo da jam’iyyar gaba ɗaya. A kusan kowane taro da majalisa, Pantami da jam’iyyarsa su ne abin tattaunawa. A cewarsu, bai k**ata a bar wannan yanayi ya ci gaba ba.

Abin takaici a gare su, sun manta cewa ikon Allah ne kaɗai ke tabbatar da abin da zai kasance.

3. A yayin da Malam Isa Ali Pantami ke ci gaba da gabatar wa al’ummar Gombe manufofinsa da kuma “Tsarin Sauya Fasalin Jihar Gombe” a fannoni k**ar noma, samar da ayyukan yi, tsaro, ilimi, mata, matasa, masana’antu da sauran su, har yanzu ‘yan takarar su ba su gabatar wa jama’a wata cikakkiyar manufa ko tsari ba.

An ce an yi wa dukkan ‘yan takarar da s**a halarci taron tambayoyi kan wannan batu. A yau, Pantami ya zama abin koyi a gare su ta wannan fuska.

Mu ci gaba da lura da abubuwan da suke faruwa yayin da al’amura ke ƙara bayyana.

Allah Ya rushe duk wani mugun nufi da mugun shiri da ake yi wa al’ummar jihar Gombe da kuma duk wani abu da zai hana samuwar shugabanci Nagari a jihar.

Rubutawa:
Barrista Yahaya Ibrahim
03/Yuni/2026

Wasu Abubuwa 10 Da Zaisa Kaso Sheikh Pro. Isa Ali PANTAMI ✅Yana Ilimin Addini Mai Tarin Yawa Da Tsoron ALLAH Saboda Haka...
30/05/2026

Wasu Abubuwa 10 Da Zaisa Kaso Sheikh Pro. Isa Ali PANTAMI

✅Yana Ilimin Addini Mai Tarin Yawa Da Tsoron ALLAH Saboda Haka Zaifi Gujewa Zalunci.

✅Yana Da Sanin Haqqoqin Jama'a a Musulunci.

✅Yana Iya Bambance Halal Da Haram Wajen Mulki.

✅Yana Da Damar Yin Hukunci Cikin Adalci Bisa Koyarwar Addini.

✅Yana Iya Karfafa Tarbiyya Da Kyawawan Dabi'u A Cikin Al'umma.

✅Zai Gudanar Da Mulki Ta Hanyar Da Ya Dace Batare Da Ashararanci Ba.

✅Zaifi Tunanin Lahira Da Alhakin Dake Kansa, Ba Duniya Kawai Ba.

✅Yana Iya Hada Kai Tsakanin Malamai Da Talakawa Cikin Sauki.

✅Addini Yana Koya Masa Tausayi Da Hakuri Wajen Jagoranci.

✅Tunda Yana Da ilimi Da Kwarewar Shugabanci Zaifi Iya Kawo Cigaba Mai Amfani Ga Jama'a.
Umar B Umar
muna fatan in sha Allah badi iwar Haka muna jaji birin rantsar da mlm binizinillah

Ziyarorin wasu daga cikin Alarammomi, da Alkalai da Limamai zuwa ga Professor Isa Ali Ibrahim Pantami domin gaisuwa da f...
30/05/2026

Ziyarorin wasu daga cikin Alarammomi, da Alkalai da Limamai zuwa ga Professor Isa Ali Ibrahim Pantami domin gaisuwa da fatan alheri da goyon baya.
Muna rokon Allah Ya mana jagoranci a dukkan al'amuranmu.

Hakika. Rayuwa tana tafiya da sauri, kuma kowannen mu zai gamu da Allah wata rana. Yin hisabi ga kai yana taimakawa mutu...
30/05/2026

Hakika. Rayuwa tana tafiya da sauri, kuma kowannen mu zai gamu da Allah wata rana. Yin hisabi ga kai yana taimakawa mutum ya gyara halinsa, ya ƙara alheri, ya guji abin da zai cutar da shi a duniya da lahira.

Kamar yadda ake cewa:
“Mai hankali shi ne wanda yake duba abin da ya aikata kafin a tambaye shi.”

Allah Ya sa mu kasance cikin masu tunani, masu gyara kura-kuransu, kuma Ya ba mu kyakkyawan ƙarshe.

Allah ka karawa Mal. IMANI da Nissan kwana Amin.

30/05/2026

ZAƁIN AURE

Duk mai son ya auri mace, ya buɗe ido ya kalli waye mahaifinta, waye ɗan’uwanta, da irin tarbiyyar gidansu. Domin sau da yawa mace tana ɗaukar halaye da dabi’u daga muhallin da ta taso. Kuma wata rana za ta iya haifa maka ‘ya’ya masu k**a da ɗaya daga cikin iyayenta ko ‘yan’uwanta a ɗabi’a da hali.

Amma kuma ya k**ata a tuna cewa:
Ba kowane mutum ne yake zama kwafin iyayensa ko danginsa ba. Addini, tarbiyya, ilmi, da kyawawan halaye suna iya canza mutum ya fi iyalinsa nagarta.

Shi ya sa addinin Musulunci ya fi ƙarfafa:

* Addini
* Tarbiyya
* Kyawawan ɗabi’u
* Hankali da mutunci

Annabi ﷺ ya ce:

“Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi’arsa ya zo muku, ku aura masa.”

Saboda haka, auren nagari yana buƙatar:

* Kyakkyawan asali
* Kyawawan ɗabi’u
* Tarbiyya
* Tsoron Allah
* Fahimtar juna da mutunta juna

Domin gida mai albarka ba asali kaɗai yake ginawa ba, har da kyakkyawan hali da tsoron Allah.

YAYYANKIWAN JINI.TAMBAYA:Assalamu Alaikum. Malam matata ta haihu sati biyu (2) kenan, to Malam yanzu takan wuni jini bai...
30/05/2026

YAYYANKIWAN JINI.

TAMBAYA:
Assalamu Alaikum. Malam matata ta haihu sati biyu (2) kenan, to Malam yanzu takan wuni jini bai zo ba, sai da daddare in ta kwanta sai jinin yazo, to shin Malam za ta iya yin Wanka da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i? Ko kuma yaya za tayi? Nagode Allah ya ƙara illimi mai albarka.

AMSA:
To ɗan uwa, a zance mafi inganci duk Yinin da ta ga jini to yana ɗaukar hukuncin jinin biki ne, haka ma tsarki yana ɗaukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za tayi wanka duk yinin da bata ga jini ba, sai dai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta haɗa sallolin da bata ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "Bai sanya muku ƙunci a cikin addini ba.", Suratul Hajj: 78.

Don neman ƙarin bayani: duba Almugni na lbnu Khudaamah (1/214). Allah ne mafi sani.

WhatsApps Group;
https://chat.whatsapp.com/JsI0zww5r9p2cod8GIE38O
_
~𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂.

WhatsApp Group Invite

TALAKAWA FA BA MUTUMEN KIRKI SUKE SO YA MULKE SU BA A NIGERIA: Case ɗin Gombe yaishi kowa ayaDuk dai ƙiyayyar ka da Pant...
26/05/2026

TALAKAWA FA BA MUTUMEN KIRKI SUKE SO YA MULKE SU BA A NIGERIA: Case ɗin Gombe yaishi kowa aya

Duk dai ƙiyayyar ka da Pantami, ƙarya kake kace masa jahili, ko bai san me ya keyi ba, kuma duk rashin mutun cin ka, da rashin son gaskiyar ka, ƙarya kake kace wai 'yan siyasar Nigeria sun fishi ƙima da mutunci.

Kome son ranka indai shugaba a ke nema, wanda zai mulki al'umma, wanda a ke kyautatawa zato ga abun da ya bayyana ga mutane, ya cancanci ya zama shugaba, fiye da shuwagabannin da suke mulkin mu a yanzu, kai harda waɗanda s**a mulkemu a baya, kai kasan Pantami ya cancanta.

Ilimi dai yana dashi, babu wanda yake gardama ko tababa a kan wannan, ya nada ilimin addinin sa (na musulunci) garau, wannan ko shakka babu, don bar waɗanda ba suje islamiyya ba sun yarda ya nada ilimin addini.

Sannan ya nada ilimin boko, wanda da yawa wasu wawaye ma ke ɗaukar wanda bai da ilimin boko a matsayin jahili ko wawa, to Pantami yana dashi.

Mutun dai ko Professor na wasa kaji 'yan ajin su a makaranta suna kiran sa, I'm telling you ya karantu, kuma ya cancanci su nan ne, bare Professor ɗin da jami'a a Nigeria tace Professor ne.

Koba Professor bane, yau dai duk wanda dai yayi Phd. ya wuce jahili, in kana ganin abun ƙarya ne, kaje kace za kayi Phd. ka gani da idanun ka.

So, ace in banda dai Nigeria na Nigeria, wai mutum irin Professor Isah Ali Pantami, wai har wani yafito yace maka wai bai cancanci ya zama shugaba ba.

A irin jahilan shuwagabannin da suke mulkin Nigeria, masu Secondary Certificates, waɗanda Fatiha basu iya ba, da waɗanda ba'a masan ina su kayi karatu ba, karatun bokon ma fa, bana addini ba, wai a irin wannan ƙasar wani ke faɗar wai irin Pantami bai cancanci shugabanci ba.

Na taɓaganin wani yana cewa, "wai ai idan ana maganar mulki, ba maganar ilimi a keyi ba", kuma wai intellectual mutun ne, fisabilillahi, to idan ana maganar mulki maganar me a ke ? Jahilci ? Ko Jagaliyanci ?

Gaskiya guda ce, na sha faɗa, duk lalacewar Pantami, na rantse da Allah yafi waɗannan shuwa

Address

Fish Market, Apo Resettlement, Abuja
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MAI AGOGO posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category