BALGANU-Hausa

BALGANU-Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from BALGANU-Hausa, Grocers, Balganuhausa, Bauchi.

Ana ta cece-kuce kan masu buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da mulki da kuma masu buƙatar ya tafi ya ba...
17/09/2026

Ana ta cece-kuce kan masu buƙatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da mulki da kuma masu buƙatar ya tafi ya bawa wani, shin mene ne matsayar ku?

TURƘASHI: Da A Ce Ka Yi Aure Ka Haifi Ƴaya Irinsu Rarara Da Musa Mai Sana'a Gwara Ka Mutu Kana Yin Istimna'i, Cewar Mata...
18/06/2026

TURƘASHI: Da A Ce Ka Yi Aure Ka Haifi Ƴaya Irinsu Rarara Da Musa Mai Sana'a Gwara Ka Mutu Kana Yin Istimna'i, Cewar Matashiya Fatima Jalal

Me za ku ce?

DA DUMI-DUMI: NDC ta hana Kwankwaso yin takara a 2027, Ta ce Dan Kudu ne kawai ke da damar yin takarar shugaban kasa a j...
09/05/2026

DA DUMI-DUMI: NDC ta hana Kwankwaso yin takara a 2027, Ta ce Dan Kudu ne kawai ke da damar yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar

Jam'iyyar NDC na gudanar da babban taron ta na kasa a yau Asabar, sai dai a yayin taron, Jam'iyyar ta ayyana cewa ta yanke hukuncin Dan yankin Kudu za ta baiwa takarar shugabancin kasa a 2027 kuma an amince da matakin,

Wannan dai na nufin tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ba zai samu damar takara a NDC din ba saboda wannan matsaya da aka cimmawa,

Wacce shawara za ku bashi?

Dan Allah ku taya mu da sharing zuwa groups...
Sanarwa domin samun ingantattun labarai kuyi Following na:

01/04/2026
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Hakan (ICPC) ta fitar da sanarwar cewa Malam Nasiru...
19/02/2026

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Hakan (ICPC) ta fitar da sanarwar cewa Malam Nasiru El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, yana hannun hukumar har zuwa karshen aiki na ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

Hukumar ta bayyana haka a shafinta na Facebook.

Malam Nasiru El-Rufai na tsare a hannun hukumar ne dangane da binciken da ake gudanarwa.

Wannan cin mutuncin Addini ne, "Baki taba fitowa kin fadi alkairin Pantami ba. Tun fara siyasarki baki taimaki addini ko...
14/02/2026

Wannan cin mutuncin Addini ne, "Baki taba fitowa kin fadi alkairin Pantami ba. Tun fara siyasarki baki taimaki addini ko 'yan Arewa da komai ba, sai zage-zage da cin mutunci" - Sheikh Salihu Zariya ga Naja'atu.

Me zaku iya cewa?

Ga Video Link 👇
https://www.facebook.com/reel/4161893524123088/?app=fbl

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa sun yi alakwarin zaben Shugaban Kasa Bol...
10/02/2026

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa sun yi alakwarin zaben Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Tabbas, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan salon hirarrakin da fitacciyar ’yar jaridar BBC Hausa, Ais...
29/01/2026

Tabbas, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan salon hirarrakin da fitacciyar ’yar jaridar BBC Hausa, Aisha Madina Maishanu, ke yi da manyan ’yan siyasa a Najeriya.

Muhawarar ta taso ne bayan wasu hirarraki da ta gudanar a baya-bayan nan, inda wasu ke sukar yadda take gabatar da tambayoyi kai tsaye tare da murtuke fuska, suna mai cewa hakan na iya shafar yadda baƙin na ta ke bayyana ra'ayoyinsu.

Sai dai wasu kuma na kare salon nata, suna cewa wannan tsari na daga cikin ƙa’idojin aikin jarida na ƙwararru.

Masu kare Madina na cewa aikin jarida ba na faranta rai ba ne, illa neman gaskiya da wakiltar muradin al’umma, musamman wajen fuskantar masu riƙe da madafun iko da tambayoyi masu zafi.

A gefe guda, masu sukar nata na ganin cewa salon hirar da murtuke fuskar da ta ke yi na iya taka rawa wajen samar da yanayin da zai hana baƙin na ta damar yin bayani cikin walwala.

Muhawarar dai na nuna yadda ake ci gaba da samun ra’ayoyi mabanbanta kan yadda aikin jarida ya kamata ya kasance a wannan zamani.

Ku bayyana ra'ayoyinku...

DA ƊUMI ƊUMI:Yadda Al’ummar garin Tidibale Dake Karamar Hukumar Isa A Jihar Sokoto Suke Kaura Bayan Wa'adin Da Bello Țùŕ...
17/01/2026

DA ƊUMI ƊUMI:Yadda Al’ummar garin Tidibale Dake Karamar Hukumar Isa A Jihar Sokoto Suke Kaura Bayan Wa'adin Da Bello Țùŕji Ýa Ba Šu Ña Barin Garin

Daga Muhammad Kwairi Waziri.

Hadimin shugaban ƙasa Tinubu, Abdul'aziz Abdul'aziz ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook...
14/01/2026

Hadimin shugaban ƙasa Tinubu, Abdul'aziz Abdul'aziz ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Bayanin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ke shirin sauya sheƙa zuwa APC.

Address

Balganuhausa
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BALGANU-Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category