ABBA Freedom.

ABBA Freedom. for the people

29/05/2026
29/05/2026
29/05/2026

Da alama rikicin siyasa na shirin ɓarkewa a tsakar gidan shemar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, tun bayan da a Larabarnan ya yi wa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna tayin takarar Sanata, maimakon takarar gwamna da Gawunan da magoya bayashi s**a jima da akan wannan tsammani.

Rahotannin cikin gida dai sun shedawa kafar Lumana radio cewar Kwankwaso ya yi wani zama na musamman na wasu daga cikin masu ruwa da tsakin tafiyar tashi tun a daren talata, kafin a ranar Laraba ya yi babban zama da ya shedawa taron shirinshi na ba wa Gawuna takarar Sanatan Kano ta Tsakiya ko kuma Mataimakin Gwamna a jam'iyar NDC a kakar zaɓen 2027.

Sai dai nan take majiyoyinmu su ka ce Gawunan ya maida tayin, in da ya nuna madamar ba takarar gwamnan Kano Kwankwaso ya bashi ba, to ba ya buƙatar yin kowace takara, amman zai goyi da bayan da baya gudunmowar samun nasarar tafiya.

An dai jima ana ta dakon matsayar Kwankwaso akan wanda zai bai wa takarar gwamnan Kano, tun bayan da ragowar jam'iyu su ka fitar da 'yan-takarkarunsu, lamarin da ya jawo ake ta zaman ɗar-ɗar a tsakanin manema takara.

Dr. Nasiru Gawuna dai ya bar APC ne da muƙamin Manajan Bankin Kasuwancin Najeriya da Tinubu ya bashi, sakamakon rashin samun tikitin takarar gwamna da ya hango.

Komawarshi wajen Kwankwaso, ya sa ana ta tunanin shikenan tsohon gwamnan ya samu ɗan-takara mai tsarin siyasarshi (structure) a ƙasa, da har ya fara taka rawa a fakaice matsayin wanda zai wa Kwankwason takarar gwamna.

Ko a bayanan da Gawunan ya yi lokacin da Kwankwason ya je ba shi katin rijistar jam'iyar ADC da su ka baro, anji yadda tsohon mataimakin gwamnan yake nuna ba zai ci amanar Kwankwaso ba idan ya bashi dama, lamarin da ke nuna Gawunan ya riga ya gama sa ran shine ɗan-takarar da Kwankwason zai ɗauka.

Wannan ta-leƙo-ta-koma dai da ake ga iwa na neman samun Gawunan, ƙila ya buɗe ƙofar fara rikicin cikin gida a Kwankwasiyya, a lokacin da dama 'yan APC s**a jima suna yi wa Gawunan je ka ka gani tun bayan da ya barsu.

Address

No 26 Maidiguri Road
Bauchi
740002

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ABBA Freedom. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category