10/09/2026
KUNGIYAR HAƊAKAR ’YAN KASUWA TA ZIYARCI MA’AIKATAR CO-OPERATIVE & SME DEVELOPMENT TA JIHAR BAUCHI.
Kungiyar Haɗakar ’Yan Kasuwa da Masu Sana’ar Hannu ta Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Hon. Abdullah Caps, ta jagoranci tawagar ’yan kasuwa zuwa Ma’aikatar Co-operative & SME Development ta Jihar Bauchi domin gudanar da ziyarar taya murna tare da ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa domin ci gaban harkokin ’yan kasuwa.
A yayin ziyarar, Kungiyar Haɗakar ’Yan Kasuwa ta yi kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi da ya ƙara waiwaye kan halin da ’yan kasuwa ke ciki tare da tallafa musu da jarin kasuwanci, domin bunƙasa sana’o’insu da kuma inganta tattalin arzikin Jihar Bauchi.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Co-operative & SME Development, Hon. Madaki Ahmad Gololo, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa da wannan ziyara da Kungiyar Haɗakar ’Yan Kasuwa ta kai masa.
Ya kuma yaba da wannan kyakkyawan yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati da ’yan kasuwa, tare da tabbatar da cewa Ma’aikatar za ta ci gaba da yin aiki tare da ƙungiyoyin ’yan kasuwa domin samar da ci gaba mai ɗorewa.