Oroba Farms Zagga

Oroba Farms Zagga Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Oroba Farms Zagga, #80, Nasarawa area, Zagga, Bagudo LG, Birnin-Kebbi.

29/10/2025

16/09/2024



♨️Duk shugaban da zai ɗauko haƙƙin wani gari, sai ya kawo shi garinsu, toh Azzalumi ne ba mai kishin gida ba.

♨️Duk shugaban da zai ɗauko haƙƙin ƴan wata ƙungiyar addini, sai ya kawo ma ƴan ƙungiyarsu, toh Azzalumi ne ba mai kishin ƙungiya ba.

♨️Duk shugaban da zai ɗauko haƙƙin ƴan mazaɓarshi, ya raba ma ƴam'iyyarshi kawai, toh Azzalumi ne ba mai kishin jam'iyya ba.

Adalci shi ne ba da haƙƙi ga ma'abutanshi ba tare da la'akari da tarayya ko saɓani ba.

Ya ALLAH Ka shirya shugabanninmu, ka sa su zama adilai

Ya Allah ba mu da wata ƙasa Najeriya, amma Najeriyar kullum ƙara rikicewa take yi, Ya Allah Ka shirya muna ita, Ka shiry...
28/08/2024

Ya Allah ba mu da wata ƙasa Najeriya, amma Najeriyar kullum ƙara rikicewa take yi, Ya Allah Ka shirya muna ita, Ka shirya shugabanninta, Ka shirya maamanta, Ka shirya ƴan kasuwarta, Ka shirya matasanta, Ka shirya yaranta da tsofaffinta, Ka shirya mazanta da matanta, ka shirya ma'aikatanta.
Allah Ka ƙarfafa fasahohin ƙirƙire-ƙirƙiren zamani a cikinta.

21/08/2024

Ya Allah duk shugaban da sakacinshi ya sa ake kashe mu da al'ummarmu, Ya Allah ka hana shi duk abun da ya ke nema duniya da lahira.

11/08/2024

: A NEW SCAM TO CHANGE THE EXISTING ONE

Leadership has no age limit. Throughout history, we've seen leaders of all ages achieve greatness. Some have made their mark at a young age, like Alexander the Great, who conquered vast territories by 25. Others have succeeded later in life, like Nelson Mandela of South Africa at 75.

What matters most is not age, but competency. Effective leaders possess skills, wisdom, and character that inspire and guide others. Age is just a number, but impact is what truly counts. Whether young or old, leaders who demonstrate ability and vision can achieve remarkable things.

shine your eyes

31/07/2024

Allahu Akbar, Ismail Haniyya babban kwamandan Hamaas, Allah Ya jiƙanka Ya rahanshe ka.
Mu kuma musulmi mu tsaya nan muyi ta jayayyar ra'ayoyin da muka ƙaƙaba ma kanmu (Ahlussunna, Sufiy, Shia, Qur'aniyy) har abokan jayayyarmu su ga bayan ƙarfinmu saboda rashin son junanmu.

Kalimar Shahada ita ce mahaɗarmu.
Duk mutumin da ya shaida LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM, kuma yana Sallah, kuma yana Zakka, ko da kuwa ya saɓa ma wata fahimta kaifiyya da muke da ita, toh wallahi ɗan'uwanmu ne, kuma yana da haƙƙi kan dukkan Musulmi.
In har wannan bai zama abun la'akari ba, toh walaƙanta yanzu muka fara gani.
Don Allah minenne Isra'ila cikin Gabas-Ta-Tsakiya.

Allahu Akbar Monzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama Ya riga Ya fada cewa "Abokan gabanku za su yi dirar mikiya akanku su yi muku artabu" sai Sahabbai Allah Ya yarda dasu s**a ce " Ya Ma'aikin Allah,saboda ba mu da yawa ne?" Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama Ya ce " kuna da yawa, amma yawan ku zai zama na banza (ba ya da amfani), kuma Allah zai cire ma abokan gabanku tsoronku, saboda kun sanya SON DUNIYA IDO RUFE a gabanku"

WALLAHUL MUSTA'AN

30/07/2024

-

In an dubi ta ɓarawo, a dubi ta mabiyi sawu

50/100

23/01/2024

LAILAHA ILLALLAH, MUHAMMADUR RASULULLAH. (Sallallahu alaihi Wasallam)

Wannan kalmar, duk wanda ya yarda da ita, toh yana da alfarma ga sauran waɗanda s**a yarda da ita, ko da kuwa saɓanin fahimtar wata matsala ya tsananta a tsakaninsu.
Don haka, duk yanda wani ya taɓa ka, toh sai ka yi mai alfarma gwargwadon riƙonshi da wannan kalmar.

Daga ƙarshe, ya k**ata mu sani, gwargwadon aikinka da wannan kalmar, gwargwadon ƙarfin imaninka, haka ma, gwargwadon saɓawa wannan kalmar, gwargwadon raunin imaninka.

Ya Allah Ka ƙarfafa imaninmu.

16/01/2024

Bismillah, Alhamdu lillah, Wassalamu ala Rasulillah bayan kaha:
Jama'a ina son in yi muna jan hankali game da abubuwan da suke faruwa a kwanan nan game da maganar , abun lura da nike son in yi magana kansu guda uku ne k**a haka:
1. Idan aka ji fatawa baƙuwa, daga wani malami, toh malamai masu irin matsayin malamin mai fatawar a ilimi ne ke da haƙƙin shiga cikinta domin tattauna ta, ba gama garin jama'a ba.
2. Ya k**ata mu riƙa yi wa malamai adalci: idan mun ga abun da zai amfani mutane daga wa'azi mu yaɗa shi, ba wai sai mun ji abun da zai kawo rabuwar kai ba kawai, mu yanke mu yaɗa don nuna kasawarshi ko kasawar ƙungiyarshi ba.
3. Ya k**ata mu bambanta abun da za'a iya faɗarshi ga ɗaliban ilimi a wurin karatu da kuma abun da za'a faɗa a wurin nasihar gama-garin jama'a.

Daga ƙarshe wannan rubutun ba ya nuna matsayina kan maganar Da aka yi, Domin fagen manyan malamai ne.
Allah Ya ba tabbatar da mu kan daidaitaccen tafarki.
Assalamu alaikum.

For your bulk supply of maize, paddy or soybeans, sorghum, kindly slide to WINICH FARMS. we deliver nationwideFor more i...
18/12/2023

For your bulk supply of maize, paddy or soybeans, sorghum, kindly slide to WINICH FARMS.
we deliver nationwide
For more info, call or Whatsapp: 07064414080

12/10/2023

Subhanallah!
Ƴan uwa mu yi ta addu'a ga Musulman Hamas dake fuskantar matsi daga kasar Isra'ila, Amurka, Faransa da sauran makiya addinin Musulunci na duniya.
Na san da yawa muna ganin k**ar su Hamas su s**a tsokani Isra'ila, ba ta reda la'akari da irin masifun da Isra'ila ke gana musu ba a tsawon shekaru kuma Isra'ila ba su bari ba har zuwa ranar da Hamas ta yi wannan martanin.
Isra'ila tana yima matan Falasɗinu fyade, tana kashe yara ƙanana, tana ƙona gidajen fararen hulla da masallatan Falasɗinawa, tana gurɓata muhallin Falasɗinawa, tana bautar da matasan Falasɗinawa, tana tilasta yara barin addinin Musulunci da dai ma wasu Abubuwan da sun ƙazamta sosai ba zan iya rubuta su ba.
Amma al'ummar musulmi duk mun yi shiru k**ar ba'a Filasɗinu masallacin Al- Aqsaa mai mataki na farko a musulunci bayan haramin Makka da na Madina yake ba.
Kowa wai tsoron yake ace masa mai zazzafan ra'ayi, ko kuma abokansa ko mabiyan shafinsa su ɓalle masa. Wannan shi ne ma'anar raunin imani a aikace.
Ya Allah Ka tsiratar da Falasɗinawa daga azzaluman duniya, Ka nuna buwayarKa da iyawarKa ga addinin Musulunci, ya Allah Ka ruɗar da azzaluman su riƙa kashin junansu da nufin kashin Musulmi, Ya Allah Ka amintar Musulmi a duk inda suke a duniya kuma rahamshe da duk mamatansu.

-Muhsin Usman Zagga
11th October 2023

03/07/2023

Alhamdu lillah

Address

#80, Nasarawa Area, Zagga, Bagudo LG
Birnin-Kebbi
871104

Telephone

+2347064414080

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Oroba Farms Zagga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share