Garko Kwankwasiyya Social Media

Garko Kwankwasiyya Social Media Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Garko Kwankwasiyya Social Media, Grocers, Garko Local Government, Dal.

Yau ne aka gudanar da gagarumin taron kaddamar da Dan Takarar Majalisar Jiha na Jam’iyyar NDC a Karamar Hukumar Garko, w...
29/05/2026

Yau ne aka gudanar da gagarumin taron kaddamar da Dan Takarar Majalisar Jiha na Jam’iyyar NDC a Karamar Hukumar Garko,

wato Hon. ABDULMALIK IDRIS GARKO,

tare da halartar manyan shugabanni da mukarraban Jam’iyyar NDC Kwankwasiyya na Garko.

Daga cikin wadanda s**a halarci taron akwai:

Jagoran Jam’iyyar NDC Kwankwasiyya na Garko

Shugaban Jam’iyyar NDC na Garko

Shugaban Dattawan Jam’iyyar NDC na Garko

Wakilin Hukumar Zabe ta Kasa

Jami’an Tsaro

Da sauran shugabannin Jam’iyyar NDC Kwankwasiyya na Garko

An kaddamar da

HOH. ABDULMALIK IDRIS GARKO

a matsayin Dan Takarar Majalisar Jiha karkashin Jam’iyyar NDC a Karamar Hukumar Garko.

Taron ya samu halartar kungiyar Garko Kwankwasiyya Social Media (GAKSOM),

inda aka nuna cikakken goyon baya da hadin kai domin tabbatar da nasarar Jam’iyyar NDC a zabe mai zuwa.

29, May, 2026.
✍️ Garko Kwankwasiyya Social Media ❤️❤️❤️ Rabiu Musa Kwankwaso

Jiya, 19 ga watan Mayu, a Abuja, na halarci tantancewar ‘yan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyarmu ta shirya, wacce ta ɗa...
20/05/2026

Jiya, 19 ga watan Mayu, a Abuja, na halarci tantancewar ‘yan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyarmu ta shirya, wacce ta ɗauki sama da awa biyu da rabi. Sun duba dukkan takarduna cikin tsanaki, ciki har da shaidun digirina, takardun NYSC, da bayanin shekaruna.

A yayin tantancewar, na kuma amsa tambayoyi game da hangen nesana na sabuwar Najeriya da irin shugabancin da ƙasarmu ke buƙata cikin gaggawa a wannan lokaci.

Bayan haka, an tantance ni tare da amincewa da ni, sannan aka ba ni fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa wanda tun farko na biya kuɗinsa.

Ina yaba wa kwamitin tantancewar ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Sam Egwu bisa ƙwarewa da gaskiyar aikin da s**a gudanar. Haka kuma, ina gode wa shugabannin jam’iyyarmu saboda tabbatar da bin tsarin dimokuraɗiyya.

Sabuwar Najeriya Mai Kyau Mai Yuwuwa Ce.

🧔Mr. p. Obi

✍️ ♥️♥️♥️

5 Million Voice who came out massively these Morning to show their full support to His Excellency Sen Rabiu Musa Kwankwa...
18/05/2026

5 Million Voice who came out massively these Morning to show their full support to His Excellency Sen Rabiu Musa Kwankwaso as well as to the NDC party at large.

18, May.2026
✍️ Gaksom Media Team Garko

Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya karɓi DCP Ibrahim Musa Sumaila mai ritaya cikin girmamawa, tare da ...
17/05/2026

Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE,

ya karɓi DCP Ibrahim Musa Sumaila mai ritaya cikin girmamawa, tare da rakiyar Hon. Ibrahim Ma’aji Sumaila da Hon. Habibu Me Lemu,

waɗanda s**a jagorance shi zuwa ziyarar ban girma inda aka karɓe shi a hukumance cikin tafiyar NDC Kwankwasiyya

a gidan Sanata Kwankwaso da ke Jihar Kano.

17, May. 2026
✍️ GAKSOM MEDIA TAEM GARKO ♥️♥️♥️

Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, a yau Asabar, 16 ga Mayu, 2026, ya jagoranci wani babban taron shugaba...
16/05/2026

Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, a yau Asabar, 16 ga Mayu, 2026, ya jagoranci wani babban taron shugabannin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na Jihar Kano a gidan sa da ke Miller Road, Kano.

Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyya domin tattauna muhimman batutuwan jam’iyya da dabarun ƙara ƙarfafa tafiyar jam’iyyar a faɗin jihar da ƙasa baki ɗaya.

✍️ Garko Kwankwasiyya Social Media

Rabiu Musa Kwankwaso Tare Da jagoranci na Peter Obi, a yau Alhamis, 14 ga Mayu, 2026, sun gudanar da wani babban taro ta...
14/05/2026

Rabiu Musa Kwankwaso Tare Da
jagoranci na Peter Obi, a yau Alhamis, 14 ga Mayu, 2026,

sun gudanar da wani babban taro tare da shugabannin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na jihohin Arewa 19,

tare da manyan jiga-jigan jam’iyyar da kuma mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa masu wakiltar jam’iyyar,

a gidansa da ke Maitama, Abuja.
Taron mai muhimmanci ya mayar da hankali ne kan hanyoyin dabaru domin bunƙasa, haɗin kai da nasarar jam’iyyar a faɗin ƙasar nan.

14, May.2026
✍️GAKSOM MEDIA TAEM GARKO ♥️♥️♥️

Na ji daɗin halartar taron farko na babban taron ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), wanda ya kasance t...
10/05/2026

Na ji daɗin halartar taron farko na babban taron ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC),
wanda ya kasance tarihi.

Taron ya haɗa mambobin jam’iyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan, inda aka nuna haɗin kai mai ƙarfi da kuma jajircewa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.

Na amince gaba ɗaya da matakin jarumtaka na jam’iyyar na ware tikitin shugabancin ƙasa ga yankin Kudancin Najeriya na wa’adin shekaru huɗu, matakin da ke ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa da tabbatar da adalci.

Ina yaba wa Jagoran Ƙasa, Sanata Seriake Dickson, bisa shirya wannan taro cikin tsari mai kyau da tasiri.

Haka kuma ina miƙa godiya ta musamman ga sauran ‘yan jam’iyya, musamman ɗan’uwana, Mai Girma Peter Obi, da kuma ƙungiyar Obidient Movement, bisa ƙawata taron da kuzari da farin jini.

Tare za mu dawo da bege, mu ƙarfafa haɗin kai, kuma mu gina kyakkyawar makoma ga ƙasarmu. - RMK

10, May .2026
✍️ Gaksom Media Team Garko

SAKO NA MUSAMMAN DAGA SHUGABANCIN KUNGIYAR GARKO KWANKWASIYYA SOCIAL MEDIA (GAKSOM)Assalamu Alaikum Warahmatullah.Shugab...
07/05/2026

SAKO NA MUSAMMAN DAGA SHUGABANCIN KUNGIYAR GARKO KWANKWASIYYA SOCIAL MEDIA (GAKSOM)

Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Shugabancin Kungiyar Garko Kwankwasiyya Social Media (GAKSOM)

na bayyana bukatar gudanar da zama na musamman tare da zababben Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Garko da Wudil, Abdulhakim Kamilu Ado domin tattauna wasu muhimman batutuwa da s**a shafi cigaban siyasa, hadin kai, da makomar tafiyar Kwankwasiyya a mazabunmu.

Wannan bukata ta taso ne sakamakon wasu dalilai na siyasa da suke bukatar fahimta da shawara tsakanin shugabanni da matasa masu ruwa da tsaki a tafiyar mu.

Don haka, muna kira da a samar da wannan zama cikin gaggawa nan kusa, domin tabbatar da dorewar hadin kai da cigaban al’umma baki daya.

Allah Ya tabbatar da alheri, Ya kuma kara dankon zumunci da fahimtar juna a tsakaninmu.

✍️ GAKSOM:
07, May 2026

Shugabancin Kungiyar Garko Kwankwasiyya Social Media (GAKSOM)

JAGORORIN KWANKWASIYYA A GARKO SUN ZAUNA DA DAN MAJALISSAR TARAIYAJagororin Kwankwasiyya a Karamar Hukumar Garko sun gud...
29/04/2026

JAGORORIN KWANKWASIYYA A GARKO SUN ZAUNA DA DAN MAJALISSAR TARAIYA

Jagororin Kwankwasiyya a Karamar Hukumar Garko sun gudanar da wani muhimmin zama tare da Dan Majalissar Tarayya mai wakiltar mazabar Wudil da Garko a Majalisar Tarayya.

An gudanar da wannan zama ne domin tattauna muhimman batutuwa tare da cimma matsaya guda,

domin ganin an kara hada kai da kuma karfafa tsarin Kwankwasiyya a Garko.

Alhamdulillah, zaman ya gudana cikin nasara da lumana,

inda aka fara lafiya aka kuma kammala lafiya, cikin hadin kai da fahimtar juna.

📅 29, April 2026
✍️ GARKO KWANKWASIYYA SOCIAL MEDIA (GAKSOM)

Na yi matuƙar farin ciki da na halarci taron tare da manyan shugabanni da ’yan kishin ƙasa masu ƙwazo wajen kare dimokur...
26/04/2026

Na yi matuƙar farin ciki da na halarci taron tare da manyan shugabanni da ’yan kishin ƙasa masu ƙwazo wajen kare dimokuraɗiyya,

a Taron ’Yan Adawa na Ƙasa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.

Taron ya samar da muhimmiyar dama a gare mu domin mu yi magana da murya ɗaya a matsayin haɗaɗɗiyar
’yan adawa,

muna da ƙuduri mai ƙarfi na karewa da ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyyarmu.
Ina miƙa godiya ta musamman ga Gwamna Seyi Makinde bisa kyakkyawar tarba da kuma yadda ya tsara wannan muhimmin taro
cikin nagarta. -

26, April.2026
✍️GAKSOM MEDIA TAEM GARKO

Address

Garko Local Government
Dal
7464

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Garko Kwankwasiyya Social Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category