18/08/2026
Da ɗumi-ɗumi: Zaɓen Osun: Jonathan Ya Bukaci A Kafa Sabbin Iyakokin doka da zata hana Gwamnoni da Ministoci zuwa duk wata jiha a lokacin da take Gudanar zaɓe
Tsohon Shugaban Ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya yi kira da a kafa sabbin ƙa’idoji kan yadda manyan ’yan siyasa da masu riƙe da mukaman gwamnati ke gudanar da harkokin siyasa a lokacin zaɓukan gwamna.
Jonathan ya yaba wa INEC, jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa da al’ummar Jihar Osun bisa yadda aka gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin lumana.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda gwamnonin da ke kan mulki, manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyu ke taruwa a jihohin da ake gudanar da zaɓe, tare da dimbin hadimai da jami’an tsaro daga wasu jihohi.
Ya ce irin wannan yanayi da aka gani a zaɓukan Osun, Ekiti da Ondo ba abu ne da ya kamata ya zama al’ada a tsarin dimokuraɗiyya ba, domin yana iya haifar da tsoro, razana da matsin lamba ga ’yan siyasa da masu zaɓe.
Tsohon shugaban ƙasar ya tuna cewa a lokacin da yake mulki, irin wannan lamari ya faru a zaɓukan Anambra na 2013 da Ekiti na 2014, inda ya ce ya bayar da umarnin manyan shugabannin siyasa da jami’an gwamnati su fice daga jihohin.
Jonathan ya gargadi cewa idan aka bar wannan salo ya zama ruwan dare, zai iya ƙara tsananta fafatawar siyasa tare da mayar da zaɓe tamkar fafatawar neman iko maimakon neman amincewar jama’a.
Ya jaddada cewa wannan ba batun Osun kaɗai ba ne, illa dai batu ne da ya shafi makomar dimokuraɗiyyar Najeriya baki ɗaya.
Saboda haka, ya yi kira ga National Peace Committee da ta shirya taron masu ruwa da tsaki da zai haɗa da INEC, jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro, Majalisar Ƙasa, NBA, Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, ƙungiyoyin fararen hula da kafafen yaɗa labarai.
Ya ce irin wannan tattaunawa za ta taimaka wajen kafa iyakoki da ƙa’idojin gudanar da siyasa, kafin abubuwan da ake ganin ba su dace ba a yau su zama al’ada a gobe.
Dr. Goodluck Ebele Jonathan, GCFR, GCON
Tsohon Shugaban Tarayyar Najeriya (2010–2015)