Ma'arush Agro Allied and General Enterprises

Ma'arush Agro Allied and General Enterprises living by the truth, leading with honour.

Processing and selling of poultry services, agro allied products, import and export trades and general contracts, farm set-up and management, training and consultancy.

A jiya Asabar ne, 05/09/2026 Na yaye Dalibin da yazo daga Karamar Hukumar Mubi, dake jihar Adamawa. Domin koyon aiki kiw...
06/09/2026

A jiya Asabar ne, 05/09/2026 Na yaye Dalibin da yazo daga Karamar Hukumar Mubi, dake jihar Adamawa. Domin koyon aiki kiwon kaji. Inda ya shafe wata 3 Yana karatu a aikace da gwaje-gwaje. Allah Ya karawa Sana'ar mu albarka 🤲

ASSALAMU ALAIKUM ĆłAN UWA MANOMA.Da fatan Kuna lafiya da ababen kiwonku. Kafin mu shiga karatun zan dan tunatar damu cewa...
31/08/2026

ASSALAMU ALAIKUM ĆłAN UWA MANOMA.

Da fatan Kuna lafiya da ababen kiwonku. Kafin mu shiga karatun zan dan tunatar damu cewar, Day old din da muka saya 1,400 zuwa 1,500 sune a record din mu, nan da mako za'a fara fitar da Yan week's 5. In Sha Allah. Saboda haka kasuwa dole ta canzawa manomi. A mai da hankali wajen duba farm record kafin a tsaida farashin kaza.

Aƙalla kamar shekaru biyar baya kenan ina ta jaddadawa manoma muhimmancin samun ma’auni (analog scale) a gidan gona. A wasu lokuta ma nakan fadi cewar duk manomin da ma'auni a tare dashi, to bai San kiwo ba har yanzu, kullum abubuwan cigaba da zamani yake zuwa mana dasu, sau tari wasu watsi suke yi dashi. Musamman mu Yan arewa, shi yasa kullum komai namu yake tafiya cikin kwan-gaba-kwan-baya. Allah Ya kyauta. Naga wuraren da akan ma'auni ake sayar da kaza a raye, iya kudinka iya shagalinka.

A wancan lokaci wasu daga cikinmu sun saurari wannan shawarar, s**a sayi ma’auni kuma s**a fara amfani da shi. Amma wasu har yanzu suna ganin kamar ba wani abu ne mai muhimmanci ba.

A yau ina so mu fahimci abu guda:
Ma’auni ba kayan ado ba ne a gidan gona. Kayan aiki ne na yanke shakku, shawara.
Idan muna son kiwon kaji na zamani, bai kamata mu dogara da ido kawai wajen tantance nauyin kajinmu ba. Dole ne mu samu ainihin bayanai ta hanyar kididdiga. Domin manomi mai bayanai shi ne manomi da zai iya sanin:
• ko kajinsa suna girma yadda ya kamata;•
• ko abincin da yake basu yana bada sakamakon da ake bukata;
• ko akwai matsalar da ke hana girma; • da kuma lokacin da ya dace ya kai kajinsa kasuwa.•
Babu mai baka wannan sakamakon sai kana anfani da ma'auni

A yau zan kawo muku muhimmancin ma’auni guda 5, kuma ina fatan bayan wannan laccar, duk wanda bai da shi zai saka shi cikin kayan aikin gonarsa na gaba.

Muhimmancin Analog Scale a Gidan Kaji
1. Sanin ainihin nauyin kaji
Analog scale yana taimaka wa manomi ya san nauyin kajinsa a kowane mako, maimakon dogaro da kallo ta hanyar hasashe kawai. Wannan yana nuna ko kajin suna samun ci gaban da ake bukata.

2. Bibiyar girman kaji.
Idan kana auna kaji daga mako zuwa mako, za ka iya gane ko suna ƙaruwa da nauyi yadda ya kamata. Idan nauyin ya tsaya ko ya ragu, za ka iya bincikar matsalar tun da wuri.

3. Taimakawa wajen tsara abinci
Nauyin kaji yana taimakawa wajen fahimtar ko adadin feed da ake basu ya dace da makwancinsu da yanayin jikinsu.

4. Gano matsala ko rashin lafiya da wuri
Wani lokaci kaji na iya fara samun matsala kafin alamun cuta ya bayyana sosai. Idan ana auna su akai-akai, rashin ƙarin nauyi na iya zama alamar cewa akwai matsalar lafiya, ruwa, abinci ko management.

5. Taimakawa wajen yanke shawarar lokacin sayarwa
Musamman ga broilers, ma'auni yana baka damar sanin matsakaicin live weight na kaji kafin ka kai su kasuwa. Hakan yana taimaka maka wajen lissafin cost, selling price da ribar gona.

Daga karshe abin da nake son ku gane shine, “Idan ba ka auna kajinka ba, kana kallon kiwo ne da ido; amma idan kana auna su, kana gudanar da kiwo ne bisa ka'ida da bibiyar diddigi.”

Ma'arush Management take muku fatan alkhairi tare da fatan samun albarka a rayuwar mu, da Sana'ar mu. 31/8/2026 ✍️

31/08/2026

Kada manomi ya tsaya waje daya.

Ba wai muna neman mu zama manyan farmers kawai ba ne…Muna son mu gina tsarin kasuwancin poultry da zai haɗa manomi da cu...
27/08/2026

Ba wai muna neman mu zama manyan farmers kawai ba ne…
Muna son mu gina tsarin kasuwancin poultry da zai haÉ—a manomi da customer, daga farm har zuwa market.
Idan muna da production amma babu market, akwai matsala.
Idan muna da market amma babu reliable supply, akwai matsala.

Amma idan production, quality, storage, logistics da market sun haɗu—sai value chain ya zama cikakke.

Ma’arush Agro — muna gina yau saboda goben mu. In Sha Allah.

06/08/2026

Farmer baya zama cikekken farmer sai Yana halartar.

=Workshop
=Seminar
= Training

Hakan zai Kara maka sanin makamar Sana'ar ka, da kuma gogewa.

Allah Ka karawa Sana'ar mu albarka.

06/08/2026 ✍️

28/07/2026
25/07/2026

Alhamdulillah!
Kaya ya sauka lafiya.

Wanda s**a saka order su matso kusa su karbi tsuntsayensu. Duk da kasancewar akwai shara.

Location Gombe

23/07/2026

Allah Ka bamu Sa'a da rabo mai albarka 🤲

19/07/2026

Albarka da fa'idojin da kiwon kajin Noilers/ Maja ke tattare acikinsa.

Zaka reneta har ta fara kwai, zaka sayar da Kwan, zaka iya kaiwa mai injin kyankyasa domin ka samu jariran Noilers, zaka iya sakawa kajin gida su kyankyashe maka, a karshe zaka sayar da iyayen ka maye gurbi da yayan.

Wannan Wani gona ne, da muka reni Maja daga old har ta samar da wadan nan yayan. Anyi Kuma kyauta, da anfanin gida da koyayensu.

Ma'arush Agro Allied and General Enterprises management

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ma'arush Agro Allied and General Enterprises posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category