Saustin Fadakarwa

Saustin Fadakarwa كنت في الديا كانك غريب او عبر السبيل

26/07/2025

Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu🙏🙏

--------------

*🕌 *SALLAH: Ita ce ginshikin rayuwata da hanyar tsira ta* 🤲🏽*

Assalamu alaikum masu bibiyata. Ina so in tuna mana da wani abu mai muhimmanci sosai a rayuwa – *SALLAH.*

Wallahi, sallah ce ginshikin addininmu. Ita ce ke tsaftace zuciya, tana hana mutum daga aikata munanan abubuwa. Ina kiran kowa da kowa, mu tsaya da sallah da gaske, ba don mutane ba – don Allah!

*📖 Allah (SWT) ya ce:*
_"Ku tsayar da sallah. Lallai sallah tana hana alfasha da mummunar dabi’a."_
*(Suratul Ankabut: 45)*

*📜 Kuma Annabi (SAW) ya ce:*
_"Abin farko da za a fara tambayar bawa da shi ranar alƙiyama shine sallah. Idan ta gyaru, duk ayyukansa sun gyaru."_
*(Tirmidhi – Sahih Hadith)*

Sallah ba nauyi bace, amma ita ce mafita. Duk matsalarka – ko ta rayuwa, ko ta zuciya – ka fara da sallah. Allah yana sane da mu. Mu gyara.

Ku kasance da wanna shafin domin tunatarwa Monzon Allah s a w yace kutunatar domin tunatarwa yana amfanan mu'mini
25/07/2025

Ku kasance da wanna shafin domin tunatarwa
Monzon Allah s a w yace kutunatar domin tunatarwa yana amfanan mu'mini

21/07/2025

Daga mafi ɗaukakar matakan imani, shi ne ka aminta da alƙawarin Allah, fiye da amintarka da abin da kake gani garau a gabanka:

Annabi Musa (AS) yana kallon kogi a gabansa, yana ganin Fir'auna a bayansa, mutanensa sun ruɗe suna cewa: Fir'auna fa ya cim mana! Shi ke nan tamu ta ƙare!
Cikin nutsuwa, Annabi Musa ya ce musu: "Faufau! Tabbas Ubangijina yana tare da ni, zai nuna mini hanyar kuɓuta."

Ma'aikin Allah (SAW), lokacin da suke fake a kogon dutse, tare da sahibinsa Abubakar (RA), kafirai sun taso su gaba, suna nemansu ruwa a jallo don su hallaka su, s**a iso bakin kogon da s**a fake. Sahibinsa ya ce da shi: Ƴar leƙowa kaɗan za su yi, su ganmu!
Cikin nutsuwa Ma'aiki (SAW) ya ce: "Mene ne tsammaninka da mutum biyu, wanda Allah Shi ne na ukunsu?"

Idan Allah Ya nufe ka da alheri, za ka sha mamakin hanyoyin da zai buɗe maka. Daga cikin ruguntsumin ƙunci, alherinSa zai kurɗaɗo ya fito da kai zuwa yalwa. Allah Mai tausasawa ne ga bayinSa.

21/07/2025

بسم الله الرحمن الرحيم

---

*🕌 SADAQA: Tushen Albarka da Rahama 🤲🏽*

Sadaka tana daga cikin mafi girman ayyuka masu ƙarfafa zumunci da jawo rahamar Allah. Ba lallai sai kana da yawa ba kafin ka bayar – ko da kaɗan ne, idan da niyya ce mai kyau, tana da lada babba.

*🧕🏽👳🏽‍♂️ Allah (SWT) ya ce:*
_“Masu ciyarwa duka da dare da rana, a asirce da bayyane, suna da ladan su wurin Ubangijinsu. Babu tsoro a kansu kuma ba za su yi baƙin ciki ba.”_
*(Suratul Baqara: 274)*

*📖 Manzon Allah (SAW) ya ce:*
_“Sadaka tana kashe fushin Allah kuma tana kare mutum daga mummunan mutuwa.”_
*(Tirmidhi, Hadisi mai ƙarfi)*

Ka rinka ba da sadaka a duk lokacin da ka samu dama — ko da ruwa ne, ko abinci, ko sutura, ko kyakkyawar kalma. Komai da ka bayar don Allah, yana da lada mai girma.

** .

Address

Anguwa Uku Gombe Local Government
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Saustin Fadakarwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category