18/08/2026
TAWAGAR SSR/SR TAYI TARO NA MUSAMMAN DOMIN ƘARA WAYAR DA KAN JAMA’A GAME DA NASARORIN GWAMNATIN JIHAR KANO
A Yammacin Jiya Litinin, 17 ga Agusta, 2026
Shugabancin SSR/SR Forum na Jihar Kano ya gudanar da wani taro na musamman domin tsara hanyoyin da za su ƙara inganta ayyukan dandalin wajen wayar da kan jama’a game da nasarori da shirye-shiryen Gwamnatin Jihar Kano.
A yayin taron, shugabannin dandalin sun tattauna muhimman dabarun ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin mambobi, tare da samar da ingantattun hanyoyin isar da sahihan bayanai game da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da Gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa.
Dandalin ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da amfani da kafafen sadarwa da sauran hanyoyin da s**a dace wajen wayar da kan al’umma da bayyana ayyukan ci gaba da gwamnatin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke aiwatarwa domin amfanin al’ummar jihar.
Haka kuma, shugabannin sun jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin tsari, haɗin kai, jajircewa da sadaukarwa, tare da ƙarfafa mambobi wajen isar da saƙon ci gaba ga jama’a cikin ingantaccen tsari.
Taron ya kuma mayar da hankali kan shirye-shiryen da s**a shafi kamfen ɗin sake zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda aka tattauna hanyoyin ci gaba da wayar da kan jama’a da bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu.