13/05/2026
Akwai matuƙar wahala ka iya nasara a rayuwa ba tare da taimakon kowa ba. Yana da kyau ya zama kana da abokai waɗanda kuke taimakon juna, babu gasa babu hassada. Idan ka hango wata hanya wadda ka san abokinka zai ƙaru da ita, to ka jona shi. Akwai daɗi sosai ace kai da abokanka duka kuna samun nasara da ci-gaba a rayuwa.
—Isa Sadi