Duniyar Kiwo Don Riba.

Website

Duniyar Kiwo Don Riba. Kiwon Tsuntsaye da Dabbobi Domin Samun Riba 🐐 🦆

09/10/2026

� TAMBAYA DAGA WANI SABON MAI KIWO ZUWA GA MASU KWAREWA A KIWO,

Assalamu Alaikum Duniyar Kiwo Don Riba.

Ina da tambaya akan wani abu dayake damuna.

Na lura wasu mutane Geese dinsu sun fara yin kwai, amma nawafa har yanzu suna zubar da gashi sosai. Sun dade suna zubar gashin, basu fara kwai ba.

Me ya sa haka? Shin lafiya lau haka take faruwa, ko akwai abunda ban musu daidai ba?

Don Allah ina son shawarar masana.

---
Daga Duniyar Kiwo Don Riba �

Mun karɓi wannan tambaya daga ɗaya daga cikin mabiyanmu.

Mun ga ya dace mu tura ta zuwa ga ɗaukacin makiyaya, musamman masu kiwon Geese.

Masu gogewa a cikin kiwon Geese, don Allah ku taimaka wa ɗan'uwanmu da shawara.

A ra'ayinku, me ke kawo jinkirin yin kwai da yawan zubar gashi a wannan lokacin?

muna Jiranku a Comment. �

Duniyar Kiwo Don Riba - Ilimi da ƙwarewa a kiwo.

09/10/2026

⚠️ KUSKUREN DA YAWANCIN MASU KIWO SUKE YI!

Suna zuba abinci mai yawa suna tafiya.

Sakamakon?
❌ Abinci ya lalace a kasa
❌ Goose ta ci kasa da cuta
❌ Kudi ya tafi a banza

🐓🌿 Sirrin shine: Kabada kadan-kadan. Ka tsaya ka kalla.

Idan sun gama, sannan ka kara.

Makiyayi nagari ba zuba abinci yake yi ba, yana lura da yadda suke ci. 💚

08/10/2026

�� Ruwa mai datti = cuta.
Ruwa mai tsabta = lafiya.

Ka canza ruwan Goose kullum. �

08/10/2026

🐓🌿 Kada ka jira asara ta koya maka abin da lura za ta iya koya maka tun da wuri.

Ka riƙa lura da abinci, ruwa, halayen dabbobinka da canjin da ke faruwa a kullum. Wannan yana taimaka maka ka gano matsala da wuri, ka kuma ɗauki matakin da ya dace.

Makiyayi nagari ba ciyarwa kawai yake yi ba, yana lura da abin da yake kiwo. 💚

🐦 ƘARAMIN ABU NE, AMMA YANA IYA TAIMAKA WA KIWONKA SOSAI.Ba wai yawan abinci kaɗai ne ke sa tsuntsaye su yi kyau ba.Loka...
07/10/2026

🐦 ƘARAMIN ABU NE, AMMA YANA IYA TAIMAKA WA KIWONKA SOSAI.

Ba wai yawan abinci kaɗai ne ke sa tsuntsaye su yi kyau ba.

Lokacin ciyarwa, tsaftar wajen kiwo, samun ruwa mai kyau da lura da halayen tsuntsayen duk suna taka muhimmiyar rawa.

Wani lokaci, canza ƙaramin abu a tsarin kulawa da tsuntsaye na iya kawo babban bambanci.

🌱 A kiwo, kula da ƙananan abubuwa ne ke gina babban sakamako.

Duniyar Kiwo Dan Riba 🐦🌾

07/10/2026

�� MAKIYAYA, KU TAIMAKA WA WANNAN SABON MAKIYAYI! �

Wani sabon makiyayi yana son sanin irin kayan da ya kamata ya tanada wa tsuntsunsa domin yin sheƙa.

� Ciyawa? � Buntun shinkafa? � Gashin tsuntsu?

Ko kuwa a bar tsuntsu ya yi sheƙa da duk abin da ya ga dama?

� ’Yan uwa makiyaya, wace shawara za ku ba shi bisa gogewarku?

� Ku bayyana mana a comments. Amsarku za ta taimaka wa wannan sabon makiyayi da sauran masu kiwo!

akiyaya

🪿 KANA SON FARA KIWON GOOSE, AMMA KA RASA YADDA ZA KA BANBANCE CHINESE GOOSE DA NORMAL GOOSE?Wani ɗan’uwa da yake shirin...
07/10/2026

🪿 KANA SON FARA KIWON GOOSE, AMMA KA RASA YADDA ZA KA BANBANCE CHINESE GOOSE DA NORMAL GOOSE?

Wani ɗan’uwa da yake shirin fara kiwon Goose ya aiko mana da wannan tambaya, yana neman ƙarin bayani daga ƙwararrun masu kiwo kafin ya je kasuwa domin sayen tsuntsayensa.

Ya na son sanin waɗannan abubuwa:

🔹 1. Chinese Goose: Waɗanne siffofi ne s**a fi bayyana shi, musamman wajen kai, baki, wuyan tsuntsu da kuma kumburin da yake sama da bakin?

🔹 2. Normal Goose: Ta yaya za a gane shi, kuma waɗanne siffofi ne s**a bambanta shi da Chinese Goose?

🔹 3. Lokacin saye: Idan Goose ɗin ƙanana ne, ta yaya sabon mai kiwo zai iya bambance nau’ikan biyu ba tare da ya ruɗe ba?

🔹 4. Shawarar masu ƙwarewa: Wane irin Goose kuka fi ba da shawarar sabon mai kiwo ya fara da shi, kuma me ya sa?

🤝 ’Yan’uwa masu kiwon Goose, muna buƙatar gudummawar iliminku!

Ku yi mana bayani dalla-dalla, musamman waɗanda s**a taɓa kiwon nau’ikan biyu. Ku taimaka wa wannan ɗan’uwa ya fara kiwonsa da cikakken ilimi, maimakon ya je kasuwa ya sayi wani nau’in da ba shi ne yake nema ba.

Ku yi sharhi da bayanin da ya dace, domin amfanar da shi da sauran waɗanda suke son fara kiwon Goose. 🪿🌿

🚨🐦 ’YAN UWA MAKIYAYA, MUNA DA TAMBAYA MAI MUHIMMANCI A GARE KU! 🪺🔥🤔 Shin kun taɓa tunanin cewa irin kayan da tsuntsu yak...
07/10/2026

🚨🐦 ’YAN UWA MAKIYAYA, MUNA DA TAMBAYA MAI MUHIMMANCI A GARE KU! 🪺🔥

🤔 Shin kun taɓa tunanin cewa irin kayan da tsuntsu yake amfani da su wajen yin sheƙa na iya taka muhimmiyar rawa a kiwonsa?

Wani sabon makiyayi ya aiko mana da wannan tambaya, kuma muna son ƙwararrun makiyaya su taimaka masa da amsa mai gamsarwa.

🐣 TAMBAYAR ITA CE:

Wane irin kayan sheƙa ya kamata a tanadar wa tsuntsu domin yin ƙwai da kwanciya a kai?

🌿 Shin ciyawa ce? 🪶 Ko gashin tsuntsu? 🌾 Ko buntun shinkafa?

Ko kuwa ya fi kyau a bar tsuntsu ya yi sheƙarsa da duk abin da ya ga dama?

🤝 ’YAN UWA MAKIYAYA, GA DAMARKU TA NUNA ƘWAREWAR KU!

Muna son jin ra’ayoyinku da gogewarku a wannan fanni domin amsa wa wannan sabon makiyayi, tare da taimaka wa sauran masu kiwo su ƙara ilimi.

👇 Ku rubuta amsarku a comment: Wane irin kayan sheƙa kuka fi amfani da su, kuma me ya sa kuke ganin sun fi dacewa?

📢 Kada ka wuce ba tare da ka ba da gudummawarka ba. Iliminka zai iya zama amfanin wani! 🐦❤️

06/10/2026

🐓🌿 Kiwo yana da abubuwan da ido yake gani, da kuma darussan da gogewa take koya.

Duk ranar da ka lura da wani sabon abu a kiwonka, ka ƙara samun ilimi. 💚🪿

Address

Dorayi Gwazaye
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar Kiwo Don Riba. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category