29/04/2026
Alhamdulillah
A Ranar Juma’ar Da Ta Gabata, Mai Girma Hon. Muhammad MD Hassan Dan Takarar Majalisar Jiha a Karamar Hukumar Nassarawa, Ya Kai Ziyara Mazabar Tudun Wada Domin Kaddamar Da Kudurinsa Na Takara Ga Shugabannin Jam’iyyar APC.
A Yayin Wannan Ziyara, Wannan Bawan Allah Dake Cikin Hoto Ya Gabatar Da Bukatarsa Ta a Taimaka Masa Da Sabon Keke Na Guragu, Anan Take Mai Girma Hon. Ya Amsa Kuma Yayi Alkawari.
Cikin Ikon Allah, a Daren Jiya Mai Girma Dan Takarar Ya Cika Wannan Alkawari, Wannan Ke Nuni Da Gaskiya, Rikon Amana Da Kulawa Da Al’umma.
Hakika, Shugabanci Nagari Shine Wanda Ake Sauraron Jama’a Tare Da Cika Alkawari.
Muna Addu’ar Allah Ya Saka Masa Da Alkhairi, Ya Karo Dubun Nasarori.
MD Hassan Media Team.