21/08/2025
Estimate na Kudin Gina Gida Mai Girman 50*50 Da Daki 3
Idan kana shirin gina gidan mafarkinka, yana da muhimmanci ka fahimci nauyin kuɗin da ke gaba. Mutane da yawa suna ɗauka cewa gina gida yana nufin gina bulo da cement kawai, amma gaskiyar magana ita ce, akwai muhimman sassa da dama da suke jan kuɗi a ginin gida.
Ga cikakken bayani kan manyan matakan aikin gini tare da kimantaccen kuɗin da ko wanne bangare ze bukata bisa ga yadda yake a kasuwa yanzu:
1. Tushen Gida (Foundation) har zuwa DPC
–Kimantaccen kuɗi: 1.8M – ₦2.5M
2. Gina Bulo daga DPC zuwa Linta da saman linta
– Kimantaccen kuɗi: 1.5M – ₦2.2M
3. Rufin kwano ko dakin
– Kimantaccen kuɗi: 3.5M – ₦5.5M
4. Fulasta (plaster)
– Kimantaccen kudi: 2.5M – 3.5M
5. Tagogi da Ƙofofi.
– Kimantaccen kuɗi: 1.8M – ₦2.2M
6. Lantarki (Electrician)
– Kimantaccen kuɗi: ₦1.2KM – ₦1.5M
7. Ruwa (Plumbing)
– Kimantaccen kuɗi: ₦800K – ₦1.3M
8. Ƙawata Gida (Finishing)
fenti, tiles, POP, PVC,
– Kimantaccen kuɗi: ₦2.3M – ₦3.5M
9. Haka Rijiya (Borehole)
Tankin ruwa, da
– Kimantaccen kuɗi: ₦1.2– ₦1.5M
10. Soakaway
– Kimantaccen kuɗi: ₦500K – ₦800K
11. Katanga da Kofa (Fence and Gate)
Katangar bulo (kimanin mita 2.5
– Kimantaccen kuɗi: ₦1.5M – ₦2.5M
12. paking Space (Flooring da External Work)Sa interlock, gyaran magudanan ruwa, da hanyoyin shiga mota.
– Kimantaccen kuɗi: ₦800K – ₦1.2M
Wannan bayani yana taimakawa mai shirin gina gida ya tsara kasafin kuɗinsa yadda ya kamata a kowane mataki. Farashin na iya bambanta bisa wurinda za ayi gini, kuɗin aiki, ingancin kayan aiki, da tsarin gine-ginen.
ka tabbatar tuntubi ƙwararren Quantity Surveyor domin samun takamaiman lissafi kafin ka fara aikin gini.