08/06/2026
Wani jigo a tafiyar Pantamiyyah, Comrade Albishir, ya bayyana cewa al’ummar Gombe za su more ingantaccen tsaro da ci gaba idan s**a bai wa Professor Isa Ali Pantami damar jagoranci.
A cewarsa, Pantami mutum ne da ya nuna kwarewa, gaskiya da kishin al’umma, yana mai jaddada cewa dukiya da rayukan Gwambawa za su samu kariya da kwanciyar hankali a karkashin jagorancinsa.
Comrade Albishir ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi la’akari da irin gudummawar da Pantami ya bayar a fannoni daban-daban, yana mai cewa idan aka ba shi dama, zai kawo ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar jama’a a fadin jihar.