Garkuwan Hon.ALD

  • Home
  • Garkuwan Hon.ALD

Garkuwan Hon.ALD Garkuwan Hon.ALD

Jagoran Jagorori Auwal Daura . Gaisheka wakili mai amfani. ✊🏽
19/08/2026

Jagoran Jagorori Auwal Daura . Gaisheka wakili mai amfani. ✊🏽

Hon Auwal Daura inda kace muyi nanne gabas. Umarni kawai muke jira me gida. Auwal Daura Dr. Dikko Umaru Radda
19/08/2026

Hon Auwal Daura inda kace muyi nanne gabas. Umarni kawai muke jira me gida. Auwal Daura Dr. Dikko Umaru Radda

18/08/2026

Ubangidan mu abin alfaharinmu ✊🏽Auwal Daura

Wani lokaci, siyasa na iya sa al’umma ta kasa gane lu’u-lu’un da ke gabanta.Akwai mutane da ba su da mukami, ba su da ku...
16/08/2026

Wani lokaci, siyasa na iya sa al’umma ta kasa gane lu’u-lu’un da ke gabanta.

Akwai mutane da ba su da mukami, ba su da kujera, amma ayyukansu sun fi na wasu masu rike da mukamai bayyana a idon jama’a. Hon. Auwal Lawal Daura yana daga cikin irin wadannan mutane, mutumin da yake kokarin yi wa jama’a hidima ba don ya samu kujera ba, amma saboda ya yi imanin cewa hidimar al’umma nauyi ce.

Abin takaici, idan muka bari son zuciya, bangaranci ko siyasa ta rufe mana ido, za mu iya wuce irin wadannan mutane ba tare da mun gane darajarsu ba.

Kada mu bari siyasa ta sa mu rasa mutanen da za su iya kawo canjin da muke nema. Wata rana za mu iya waiwaya mu gane cewa abin da muke nema a matsayin “sabon jagora” yana gabanmu tun da dadewa—amma mun kasa ganinsa saboda hayaniyar siyasa.

Wasu mutane ba sa bukatar mukami kafin su yi wa jama’a hidima. Ayyukansu ne mukaminsu. Dr. Dikko Umaru Radda Katsina Daily News

Hon Auwal Daura wakili mai amfani mai tausayin talakawa. Muna tare dakai Hon ALD✊🏽
10/08/2026

Hon Auwal Daura wakili mai amfani mai tausayin talakawa. Muna tare dakai Hon ALD✊🏽

✊🏽
08/08/2026

✊🏽

Hon Auwal Lawal Daura( wakilin Raya Kasar Daura). Ubangidan mu mai sharewa al’umma hawaye. Umarnin ka kawai mukejira. Ya...
08/08/2026

Hon Auwal Lawal Daura( wakilin Raya Kasar Daura). Ubangidan mu mai sharewa al’umma hawaye. Umarnin ka kawai mukejira. Yadda ka dama haka zamu sha wakilin Raya Kasa Auwal Daura

Ana gina suna da kuɗi, amma ana gina tarihi da ayyukan alheri. Wannan ne ya bambanta Hon. Auwal Lawal Daura.Ta hannun AL...
05/08/2026

Ana gina suna da kuɗi, amma ana gina tarihi da ayyukan alheri. Wannan ne ya bambanta Hon. Auwal Lawal Daura.

Ta hannun ALD Foundation, ya taɓa rayuwar dubban mutane ta hanyar tallafa wa ɗalibai, marasa lafiya, mata da matasa, da kuma bayar da kayan aikin asibiti ga cibiyoyin lafiya a faɗin Jihar Katsina. Ya ƙarfafa mata sama da 500 da kayan sana’a, ya raba kayan karatu ga ɗalibai a Masarautar Daura, tare da bai wa mutane da dama jari domin fara sana’o’insu.

Saboda irin wannan hidima ce aka karrama shi da sarautar Wakilin Raya Ƙasar Daura—karramawar da ta dace da mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Ko da yake ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya, a gare mu, ya riga ya zama wakilin jama’a ta ayyukansa. Da ace Najeriya tana da shugabanni masu zuciya irin tasa, da ƙasarmu ta fi haka.

Muna alfahari da kai. Muna tare da kai. Kuma, In shaa Allah, za mu ci gaba da ba ka cikakken goyon baya.

Allah Ya ƙara maka lafiya, hikima, ɗaukaka da albarka. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi. Ameen.

Akwai mutanen da ake girmamawa saboda muƙami, amma akwai waɗanda ake girmamawa saboda ayyukan alheri. Hon. Auwal Lawal D...
05/08/2026

Akwai mutanen da ake girmamawa saboda muƙami, amma akwai waɗanda ake girmamawa saboda ayyukan alheri. Hon. Auwal Lawal Daura(wakilin Raya Kasar Daura)li na cikin irin waɗannan mutane.

Ta hannun ALD Foundation, wadda shi ne Founder kuma Chairman, an gudanar da ayyukan alheri masu tarin yawa a faɗin Jihar Katsina. An tallafa wa ɗalibai da kayan karatu, an ba mata sama da 500 jari da kayan sana’a, an ba matasa damar dogaro da kai, sannan an raba kayan aikin asibiti ga cibiyoyin lafiya a Daura, Sandamu, Mai’adua, Baure da sauran sassan jihar.

A kusan duk inda ka je a Jihar Katsina, akwai wata alama ta ayyukan ALD Foundation. Gaskiya, ayyukan alherin da Hon. Auwal Lawal Daura ya gudanar sun yi yawa fiye da abin da za a iya lissafawa.

Allah (SWT) Ya ƙara masa lafiya, hikima da arziki mai albarka, Ya ci gaba da amfani da shi wajen hidimtawa addini da al’umma. Allah Ya saka masa daDr. Dikko Umaru RaddaAmeen. Dr. Dikko Umaru Radda

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Garkuwan Hon.ALD posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed food & beverage service?

Share