02/08/2026
Malamai da yan siyasar
Arewacin najeriya!
Wannan shine taken ķasidata, a daidai Wannan lokaci.
A makonda ya wuce ķungiyar haðakar kistocin najeriya ta katolika wato (the conference of catholic bishops of nigeria) ķarķashin jagorancin. Bishop Onaiyekan tare da tawagarsa sun kaiwa mai girma shugaban ķasa ziyara a fadar shugaban ķasa dake abuja, alokacin ziyarar shugaban tawagar baiyi ķasa a guiwaba wajen sanarda shugaban ķasa mai yake tafe dasuba, a'inda ya baiyana masa cewa al'ummar najeriya suna cikin mawuyacin hali a yanzu, tun daga matsanancin yunwa, baķin talauci, da rashin tsaro, da kuma fargabanda mafi yawan ÿan najeriya suke dashi akan hukumar zaɓe ta INEC, wato ko zata kasance mai adalci akan kowa?
Allahu Akbar 😪
Wannan yana faruwane a daidai lokacin da mafi yawa daga cikin malamai da sarakuna da ÿan'siyasa da ķungiyoyi masu zaman kansu daga arewacin najeriya
Suke fitowa a fili suna gayawa jama'ar arewa dama ķasa baki ðaya cewa dole mu kuma zaɓar tinunbu don ya cancanci mu bashi dama ta biyu, saboda yayi abunda ya dace.
Duk kuwa da irin rayukan da suke sulwanta kullum ranar duniya, musamman a yankin arewa.
Sunce akwai TSARO
Duk da baķin talaucinda yake addabar talaka, musamman a yankin arewa.
Sunce akwai YALWA
DUK da irin ķabilancinda wannan gwamnatin take nunawa a fili wajen rabon albarkatun ķasa da muķamai.
Sunce akwai ADALCI
Jama'a abun dubawa anan shine, a yanzufa waðannan gurɓatattun shuwagabannin sune zasu fito suna gaya muku karku zaɓi wanda ba musulmiba ko kuma ba ðan'arewaba 🙄
Koh kuma su gaya muku cewa musulmi yafi kirista a fage na siyasa wanda Allah ya kamanta da hada hada na rayuwa, wato iya abunda zai fisheka ka tsirada rayuwarka indai bai shafi haramba.
Musali: kamar ruwan kashe gobara, a'ina akace dole sai ruwan rijiya ko na fanfo ?
ai dasu da ruwan kwata duk daidaine,
Iya abunda muke nema a siyasa shine adalci.
Kodakoh wanda zaiyi mana adalcin bashi da addini.
Don haka duk wanda ya zauna aka ci gaba da jan igiyarda aka rataya masa na ķabilanci da addini saboda son zuciyar wasu ÿan tsiraru a cikinmu a daidai wannan lokaci, wallahi shi yaso.
Kuma duk wanda yace irin masifu da bala'oin da muke gani tun daga kan mulkin mai gaskiya 😬 har zuwa yau bai'isaba, toh don Allah ta zarce.
Wannan shine abunda ya samu, sai mun ķara haðuwa a wani karon.
Jiki magayi.