25/08/2026
Gwamna Radda Ya Ƙara Kira da a Yawaita Addu’o’in Samun Zaman Lafiya da Tsaro a Lokacin Maulidi
Ya buƙaci Malamai su Ƙara Yaɗa Koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W.) da Kyawawan Halaye
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da al’ummar Musulmi da su ƙara yawaita addu’o’in neman zaman lafiya, tsaro da ci gaba a Jihar Katsina da Nijeriya baki ɗaya.
Gwamna Radda ya yi wannan kiran ne a yau a Gidan Gwamnati da ke Katsina, lokacin da ya karɓi bakuncin malaman addinin Musulunci da wasu daga cikin al’ummar Musulmi da s**a zo domin taya shi murnar Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.).
Gwamnan ya yaba wa Musulmi bisa yadda suke girmama Annabi Muhammad (S.A.W.) ta hanyar gudanar da tarukan Maulidi, karatun Ƙasidu da sauran shirye-shiryen da ke tunatar da rayuwar Annabi da koyarwarsa.
Ya bayyana cewa irin waɗannan taruka suna ba da dama wajen ƙarfafa haɗin kan al’umma, zaman lafiya da fahimtar juna, tare da ƙara himma wajen bin kyawawan koyarwar Musulunci.
Gwamna Radda ya ce:
«“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara yawaita addu’o’in neman zaman lafiya da tsaro a Jihar Katsina da ƙasar nan, tare da ƙarfafa kyawawan halaye, koyarwa da dabi’un Manzon Allah (S.A.W.).”»
Ya kuma roƙi malaman addini da su ci gaba da wayar da kan al’umma game da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W.), tare da ƙarfafa mutane su kasance masu haɗin kai, haƙuri, juriya, zaman lafiya da kyautata wa juna.
Tun da farko, Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Isyaku Dabai, ya gode wa Gwamna Radda bisa karɓar bakuncinsu, tare da taya shi murnar Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.).
Shi ma Mai Bai wa Gwamnan Shawara kan Harkokin Addini, Malam Mahi Muhammad Bello, ya bayyana muhimmancin ranar 12 ga Rabi’ul Awwal, inda ya ce ziyarar ta kasance ne domin taya Gwamnan murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W.).
Taron ya samu halartar manyan malaman addinin Musulunci, jami’an gwamnati da kuma wasu daga cikin al’ummar Musulmi.
Shuaibu Abubakar Matazu
Media Aide to the Governor of Katsina State
25 ga Agusta, 2026