19/09/2026
Muna neman tsari a gare Ka, Ya Allah, daga ƙiyayya bayan soyayya; da gāba bayan abota; da yankewar zumunci bayan kusanci; da harara bayan fara’a da murmushi.
Ya Rahmān, Ka tsare zukatanmu daga sauyin da ba mu san yadda ya fara ba. Kada Ka bari wanda ya taɓa zama farin cikinmu ya zama abin takaici gare mu; kada Ka bari soyayyar da ta haɗa mu ta koma ƙiyayyar da za ta raba mu.
Ka dawwamar da alheri a tsakaninmu, ko da hanyoyinmu sun rabu. 🤲