25/08/2026
KUNGIYAR J.HEALTH STAFF DA CASUAL STAFF NA KARAMAR HUKUMAR RONI TA JADDADA GOYON BAYAN SU GA MAL.UMAR NAMADI DANMODI FCA DA JAM’IYAR APC DAGA SAMA HAR ƘASA A ZABEN 2027, IN SHA ALLAH.
Maigirma Hon. Dr. Abba Ya'u , zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC, ya samu wakilcin Hon. Abdullahi Dam, Hon. Shehu Yusuf, P.A. ɗinsa, da Hon. Muhammad Hafizu, S.A. Health Monitoring Roni na Gwamna, inda s**a karɓi baƙuncin ƙungiyar J.Health Staff da Gwamna ya ɗauka aiki, tare da ƙungiyar Casual Staff guda 110 da Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni ya ɗauka aiki,wanda kuma yake basu alawus (Allowance) duk wata, Ƙungiyoyin,waɗanda aka ambata a sama, sun jaddada cikakken goyon bayan su ga Jam’iyyar APC daga sama har ƙasa a zaɓen 2027 mai zuwa, in sha ALLAH,
Alhamdulillah,a cewar wasu daga cikin shugabannin ƙungiyoyin J.Health Staff da Casual Staff,sun tabbatar da cikakkiyar amincewarsu da ƙudirin ganin Jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen da ke tafe, daga sama har ƙasa,sun bayyana cewa suna tare da tafiyar Jam’iyyar APC, tare da addu’ar Allah Ya ƙara ba ta nasara Amin.
Sun bayyana cewa wannan gwamnati tana tafiya ne bisa tsari mai kyau,adalci,gaskiya da amana,musamman wajen samar da ayyukan yi ga al’umma,musamman matasa da mata,domin su samu damar dogaro da kan su,wannan ne ya sa suke bayyana cikakken goyon bayan su ga wannan tafiya.
Haka kuma,sun miƙa saƙon godiyar su ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni,Hon. Dr. Abba Ya’u, bisa ƙoƙarin sa wajen kula da matasan da ke aiki a cikin asibitocin da ke faɗin Ƙaramar Hukumar Roni,sun yi masa addu’ar ALLAH ya saka masa da alheri, Ya kuma ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da hidimtawa al’umma. Amin Ya ALLAH.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Roni, da s**a haɗa da wakilan Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi FCA, wakilan Sanata Babangida Hussaini, Walin Kazaure, da wakilan ɗan Majalisar Tarayya, Engr. Ahmad Rufai Santurakin Kazaure, da kuma wakilan Hon. Lawan Muhammad Tambari, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar Roni,da sauran manyan jiga-jigan Jam’iyyar APC sai wasu dagacin shugabanni,muna roƙon ALLAH Ya ƙara haɗa kan al’ummar Roni, ya ba mu zaman lafiya da ci gaba,ya kuma ba Jam’iyyar APC nasara a dukkan matakan zaɓe na 2027 Apc daga sama har ƙasa ALLAH ya bamu nassara Amin ya ALLAH.
ABUBAKAR HARUNA BABBA
SPECIAL ADVISER ON NEW
RONI LOCAL GOVT.