Nisa,us Sunnah

Nisa,us Sunnah أنا لست بشيء🚶
لكن أنا عبدالله👌
أن الله عز وجل خلقني🧑
من ماء نطفة💧
هذاهوأصلي✊
كيف أتكبر❓
I LOVE M
أمر بالمعروف والنهي عن المنكر

Rashin Mutunci da Rashin Kunya na Wasu Matasa a Wannan Zamani 😭Abin takaici ne yadda a wannan zamani wasu daga cikin mat...
09/06/2026

Rashin Mutunci da Rashin Kunya na Wasu Matasa a Wannan Zamani 😭

Abin takaici ne yadda a wannan zamani wasu daga cikin matasa s**a mayar da shafukan sada zumunta wajen yaɗa bidiyoyi da hotunan da s**a saɓawa tarbiyya da ɗabi'un Musulunci.

Abin da a da ake ɓoyewa saboda kunya, yanzu wasu suna nunawa duniya gaba ɗaya ba tare da jin nauyin Allah ko na al'umma ba.

Allah Maɗaukakin Sarki yace:
﴿ إِنَّ الَّذِينَ يُحِبُّونَ أَنْ تَشِيعَ الْفَاحِشَةُ فِي الَّذِينَ آمَنُوا لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ﴾
"Lalle waɗanda suke son alfasha ta yaɗu a cikin muminai, suna da azaba mai raɗaɗi a duniya da lahira." (Suratun Nur: 19)

Haka kuma Annabi ﷺ yace:
"كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا الْمُجَاهِرِينَ"
"Dukkan al'ummata za'a yi musu afuwa sai waɗanda suke bayyana saɓo a fili." (Bukhari da Muslim)

Ya kamata matasa su sani cewa shahara ta hanyar yaɗa badala ba nasara ba ce, illa ce da za ta jawo fushin Allah, rushe mutunci, da lalata tarbiyyar al'umma.

Duk wanda ya taimaka wajen ɗauka, yaɗawa, ko kallon irin waɗannan abubuwa yana da nasa kaso na alhakin.

Iyaye, malamai da shugabanni suna da nauyin kula da matasa, basu tarbiyya, da kuma jan hankalinsu zuwa ga abin da zai amfane su a duniya da lahira.

Allah ya shiryar da matasanmu maza da mata, ya tsare su daga fitintinu na zahiri da na boye, yasa su zama abin alfahari ga addininsu da al'ummarsu.

Allah' kaji kan bawanka ka masa rahama..Mun amfana da karatuttukansa musamman na magaungunae da aure..
05/06/2026

Allah' kaji kan bawanka ka masa rahama..
Mun amfana da karatuttukansa musamman na magaungunae da aure..

04/06/2026
Idan kana da lokaci, ka dan koma baya ka duba tsoffin hotunan matarka na zamanin da kafin ta aure ka. Wannan kyakkyawar ...
04/06/2026

Idan kana da lokaci, ka dan koma baya ka duba tsoffin hotunan matarka na zamanin da kafin ta aure ka. Wannan kyakkyawar fuskar, kwanciyar hankalin, da tsabtar jikin... gaba daya ta sadaukar da su ne, ta rasa baccin darenta, ta shiga matsanancin wuyar raino domin kawai ka samu darajar amsa sunan Uba a idon duniya.

Don haka, kada ka taba yin kuskuren buda baki ka ce wa matarka "me kika tsinana min a gidan nan?" don kawai kana ajiye mata kudin cefane ko kana yi mata hidima. Ko nawa ne tarin dukiyarka, bashin wahalar da ta sha wajen daukar cikinka, jinin da ta zubar, da jikinta da ya lalace wajen haifar maka zuri'a, ba zaka taba iya biyan sa ba har abada. Ka rinka ba ta girma da daraja yadda ya kamata.

Masu pos kuyi hattara🤔🤔🤔Na Shiga Uku.Wani saurayi ne yazo cire kuɗi har naira dubu cas'in da shida ₦96 wajen wannan yari...
01/06/2026

Masu pos kuyi hattara🤔🤔🤔

Na Shiga Uku.

Wani saurayi ne yazo cire kuɗi har naira dubu cas'in da shida ₦96 wajen wannan yarinya mai sana'ar POS ta karɓi ATM ta saka a machine ta rubuta ₦96 ta bashi machine ya saka PIN ɗinsa.

A lokacin taje ƙirga kuɗi dubu cas'in da shida ₦96 tana kan ƙirgawa shi kuma ya riga ya gama saka PIN ɗinsa ya canja shi zuwa 9,600 ita bata ɗago ba sai bayan ƴan mintuna ta duba transaction taga Dubu tara da ɗari shida ₦9,600 ya cire a ATM ɗinsa ita kuma ta bashi dubu cas'in da shida 96.

🐚💙 Ke mai kiran saurayi marowaci don bai baki kudin lalle da kitso ba, shin mu kaddara bakida saurayi zaki zauna babu ki...
26/05/2026

🐚💙 Ke mai kiran saurayi marowaci don bai baki kudin lalle da kitso ba, shin mu kaddara bakida saurayi zaki zauna babu kitso da lallen ne kokuma zakiyi? Idan bazakiyi ba don bakida saurayi da zai baki, meyasa bazakiyi shiru kawai ki zauna haka ba?

Idan kuma zakiyi kitson duk da bakida saurayinda zai baki, tambayan shine ina zaki samu kudin? Mata kubamu amsa😀

26/05/2026

Ranar Arfa Ranace Ta Kuka Da Zubda Hawaye🥹Da Kuma Tsantsan Tawali,u Ga Allah Kada Kuyi Wasa Da Ranar Arfa Musamman Bayan...
25/05/2026

Ranar Arfa Ranace Ta Kuka Da Zubda Hawaye🥹

Da Kuma Tsantsan Tawali,u Ga Allah

Kada Kuyi Wasa Da Ranar Arfa Musamman Bayan Sallar La,asar

Ku Shige Cikin Daki Lokacin Allah Zai Sauko Saman Samar Duniya 🌎

Domin Ya Karba Kiran Bayin Sa Ya Biya Buqatun Masu Buqata Yayi Gafara Da Masu Buqatar Gafara Yayi Rahama Ga Bayinsa

Ku Dage Wannan Damace Da Take Zuwa So Guda Ashekara Babu Yini Mafi Falla Sama Ga Wayen Nan Da Muke Acikin Su Mu Samman Gobe Arfa

Kunada Buqatu Kada Kuyi Wasa Dun Allah Bayin Allah

Ina Tunatar Dakune Domin Ina Sonku Da Alkhairi Yan Uwan Musulunci

Sako Daga Group Admin
*Musa Bello Gosta✍️*

*🧕🏼Nisa,us Sunnah🧕🏼*

⬛️RANAR ARFAH⬛️♦️Mu wata al'umma ce da rayuwar mu bata da tsawo idan aka dangana al'ummomin da s**a zo kafin mu, don hak...
25/05/2026

⬛️RANAR ARFAH⬛️

♦️Mu wata al'umma ce da rayuwar mu bata da tsawo idan aka dangana al'ummomin da s**a zo kafin mu, don haka ne Allah ya chanza mana da wasu abubuwa na Alkhairai, don ya ninninka ladar mu a ciki♦️

✔️ [ Gobe Talata ita ce ranar Arfah]

◻️ Manzon Allah ﷺ ya ce:
🔺Babu wata rana da Allah yake yawan 'yantar da bayi a ciki daga wuta, kamar ranar Arfah. Kuma lallai Allah yana matsowa sannan yayi alfahari dasu ga Mala'iku, sai ya ce: Waɗannan mai suke nufi❓🔺
📜مسلم1348

◻️ Manzon Allah ﷺ ya ce:
🔺Mafi Alkhairin abin da na faɗa Ni da Annabawan da s**a zo kafin Ni: La'ilaha illallahu, wahdahu lasharika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa ala kulli shai'in Qadirr🔺 ‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍‍
📜السلسلة الصحيحة 1503

◻️ عن عمر بن الخطاب -رضي الله عنه-
"Wani mutum daga cikin Y@hud@w@ ya ce: Ya kai Shugaban Mumin@i akwai wata aya acikin littafin ku, kuna karanta ta, da ace akan mu (taron Y@hud@w@) aka saukar da ita da mun riƙi wannan rana, ranar Idi".

Umar ya ce: Wace Aya ce❓
Sai ya ce:
:🔺 اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا 🔺
[المائدة: 3]
💡Umar ya ce:
"Haƙiƙa Mun san wannan rana, da wajen da ta sauka ga Annabi ﷺ, yana tsaye a Arfah, ranar Juma'a".
📜البخاري45

___

◼️ قـال الحافظ ابن رجب -رحمه اللّٰه-:
"Ranar Arfah ita ce ranar da ake 'yantarwa daga wuta, Allah yana 'yantarwa aciki daga wuta, wanda ke tsaye a filin Arfah da wanda baya tsaye afilin, na daga mutanen birane na Musulmai.

Don haka ne ya zama ranar dake bayan Arfah ta zama ranar Idi ga dukkan Musulmai acikin dukkan Biranen su, wanda ya halarci wannan taron/tsayuwar da wanda bai halarci taron/tsayuwar ba, don su yi tarayya cikin wannan 'yantarwa da gafara a ranar Arfah".
📜كتاب : لطائف المعارف

◼️ قال عطاء -رحمه الله-:
« Idan ka samu ikon keɓance kanka a yammacin Arfah to aikata hakan »
📜الزهد للإمام أحمد (2211)

💡 "Yammacin Arfah shi ne: daga sallar La'asar zuwa kiran sallar Mangariba".

___

◻️ Allah yasa albarka cikin abin da muka rubuta ya gafarta mana kuskuren da ya auku

•┈┈•◈◉❒ 📚 ❒◉◈•┈┈•

Ka tunatar da wanin ka, domin wanda yayi nuni ga aikin Alkhairi, yana ladar wanda ya aikata.

════ ❁●✿●❁ ════

سُبحانَكَ اللهمَّ وبحَمدِكَ أشهَدُ أنْ لا إلهَ إلّا أنتَ أَستَغفِرُكَ وأتوبُ إليكَ

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nisa,us Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category