07/08/2026
YADDA ZA KI DAWO DA MIJIN KI IDAN YA JUYA BAYA
‘Yar Uwa… ki matso kusa, ki gyara zama, domin yau akwai sabon karatu—ba na fada ba ne, ba na kuka ba ne… na hikima, nishadi da dabara ne.
‘Yar Uwa, ga wani magani na musamman… amma gaskiya yana da ɗan bauri da daci 😅, kuma sharadin sa shi ne: idan kika fara, sai kin jajirce! Domin idan kina son ganin sakamako mai kyau… dole sai kin daure.
Lakabin sa kuwa shi ne: “IDAN KA JURE, KA SAMU NUTSUWA.”
Amma fa ki kwantar da hankalinki… ba na wurin boka bane 😂 domin wannan maganin ya fi karfin boka ma!
'Yar Uwa, shin wata rana kina yiwa kan ki wannan tambayoyin akan mijin ki?
😔ME YA SA YA CANZA?
Wata rana yana dariya, wata rana kuma ya zama kamar an canza masa software, baya fara’a, baya kula, komai sai ya zama fada
Sai ki ringa cewa: “Wai me na yi ne?” 🤔
To ‘yar Uwa… ki ji gaskiyar nan:
ba komai yake nufin kin yi kuskure ba.
Wasu lokutan rayuwa, damuwa, ko sabawa ne ke sa namiji ya sauya hali.
SABON KARATU (MAGANI CIKIN RUWAN SANYI)
1. KI DAN JA BAYA KADAN
Eh mana 😄 ba wai ki gudu ba ne… amma ki rage yawan bin sa da tambayoyi. Domin idan kika matsa sosai, zai kara ja baya.
“Give him space, not pressure.”
2. KI MAYAR DA GIDA “PEACE ZONE”
Kar ki kara masa hayaniya a lokacin da yake cikin damuwa.
Ki zama:
mai nutsuwa
mai saukin kai
mai murmushi
Domin gaskiya:
inda ake samun kwanciyar hankali, nan zuciya take komawa.
3. KI DAINA “OVER REACTION”
Kadan ya yi… sai ki tada hankali kamar breaking news 📢😂
A’a ‘yar uwa… ki rage haka.
wani lokacin shiru da murmushi sun fi maganganu dubu tasiri.
4. KI DAWO SABUWA
Ba wai kin canza kanki gaba daya ba…
amma:
ki kara kulawa da kanki
ki dawo da barkwanci
ki kara nishadi a gidanki
“Be the version of you he can’t ignore.”
5. KI YI AMFANI DA DABARAR “SOFT POWER”
Ba da fada ba… ba da karfi ba…
da lafazi mai dadi da kulawa ake cin nasara.
Wani lokaci ki ce masa:
“Na yi kewar yadda muke dariya da kai.”
Sai ki ga zuciyarsa ta fara motsawa a hankali.
Wata tace:😄
"Ni dai idan ya fara wani hali, nima sai na nuna masa ni ma zan iya!"
Na ce mata:
“To ai kin bude branch din fada kenan!” 😂
‘Yar Uwa… wannan ba competition bane
hikima ake bukata, ba karfin fada ba.
SIRRIN NASARA
Ki rike addu’a sosai:
"Ya Allah ka dawo da soyayya da fahimta a tsakaninmu, ka cire duk wani sabani, ka daidaita zuciyarsa gare ni cikin alkhairi."
Domin gaskiya:
akwai abubuwan da ba dabara kadai ke gyara su ba sai da taimakon Allah.
‘Yar Uwa…
kada ki gaggauta yanke hukunci
kada ki bi shi da zafi
ki yi hakuri, ki yi dabara
Domin canji ba rana daya yake zuwa ba.
“Patience and consistency bring results.”
Ki jajirce… ki yi amfani da hikima… ki tsaya da addu’a…
Sai ki ga a hankali…
zuciyar da ta juya baya… ta dawo gare ki cikin nutsuwa.💖
Allah ya tabbatar da fahimta da nutsuwa a cikin kowanne aure, AMEEN.
Masu tambaya kumin magana ta private
Group din MU na WhatsApp wacce takeso asata tamin magana ta WhatsApp