19/05/2026
KA KOYI YIN SHIRU A WASU LOKUTA.
Ba duk magana ce ake buƙatar ka mayar da martani a kanta ba. Ka sani a wani lokaci yin shiru… ya fi doguwar gardama ko jayayya amfani.
Mutum mai hankali ba ya bata lokacinsa wajen nuna wa kowa cewa shi ne a kan daidai. A rayuwa:
> Za ka haɗu da masu son tada maka hankali,
> Masu son ganin ka yi fushi,
da masu son su ja ka cikin rigima.
Amma idan ka koyi yin shiru, kau da kai da kuma nutsuwa… za ka fi samun kwanciyar hankali.
Ka sani cewa, duk wanda ya iya sarrafa zuciyarsa, ya fi ƙarfin wanda yake son ya rinjayi mutane da hayaniya.
Wani lokaci mafi girman nasara… shi ne ka wuce ba tare da ka ce komai ba.