Lokaci Baƙo Ne

Lokaci Baƙo Ne Bai kamata ba ka yi duk wani posting marar amfani ba.

22/07/2026

Lokaci 🕒 abu ne mai matuƙar muhimmanci wanda idan ya tafi ba zai dawo ba. Akwai hikima wajen amfani da shi yadda ya dace yadda zai amfane mu Duniya da Lahira.

22/07/2026

Yawan posting ɗin hotuna a dandalin sada zumunta ɗabi'a ce ta mata masu son su burge.
Daudanci ne ga namiji ya dinga yawan posting ɗin hotunanshi a dandalin.

19/07/2026

Lokaci ⌚ baƙo ne... ✍️

Yana zuwa ba tare da gayyata ba.
Yana zama kaɗan.
Sannan yana tafiya ba tare da ya ce "sai wata rana" ba.
Lokaci baya jiran kowa.

Lokaci yana bayyana ainihin mutane. Aboki na gaskiya 🤝, soyayya ta gaskiya 💞🥰, manufa ta gaskiya 🤏. Duk lokaci ne ke fitar da su.

Lokaci ⌚ yana warkarwa, amma kuma yana ƙara rauni, ya danganta da abin da ka yi da shi.
Idan ka yi amfani da shi cikin hiƙima, yana magani. Idan kuwa ka ɓata shi, yana cutarwa .

Duk abin da kake da shi yau, ba shi lokaci ⌚ 🕒
Kuɗi na iya dawowa , amma daƙiƙa ɗaya da ka ɓata ba zai dawo ba.


Kada ka ce ba ka da lokaci. Kana da lokaci iri ɗaya da wanda ya yi nasara. Tambayar ita ce: Me kake yi da shi? 👉 ⌚.

Yi amfani da lokacin yau, domin gobe ba ta da tabbas ɗin zuwa kana raye.

Allah ya albarkaci lokacinmu 🙏 💞

18/07/2026

Mafi yawan al'ummar wannan zamani duk sun zama ƴan maular zamani, da sunga Allah Ya Yi wa wani arzikin kuɗi sai kaga suna ce wa " Wane mutumin kirki ne kaza da kaza" Ana ɗora hotonshi a Facebook ana kambama shi saboda kawai ya ba su kuɗi.

16/07/2026

Wasu idan jarabawar talauci ta same su sai ta zame musu alkhairi su koma ga Allah .
Wasu kuwa sai ta zame musu sharri su yi ta shirme duk subi su firgice.

27/06/2026

Kowa sai son ya burge da nuna komi lafiya lau.

Ina ganin wautar mutane da a garinku wasu wawaye su shigo muku su dinga muku abinda s**a ga dama.Yadda kuke mutane su ma...
13/06/2026

Ina ganin wautar mutane da a garinku wasu wawaye su shigo muku su dinga muku abinda s**a ga dama.
Yadda kuke mutane su ma fa haka suke mutane. Ku kuka san garinku kuka san malaɓa, shi yaƙi ɗan zamba ne.

Kamata ya yi al'umma su cire tsoro su yi abinda ya dace don karon kansu dana iyayensu, da iyalansu, da ƴaƴansu, da duka ƴan uwansu Musulmai.

Yadda kuke tsoron mutuwa suma haka suke tsoron ta.

Da a wulaƙanta ka ka kashe ka, gara ka yi shahada wajen kare iyalinka.

SUBHANALLAH: Labarin da muke samu yanzu haka na tabbatar da wasu gungun ÿàn̈ ťà'àđđa saman babura sama da ɗari, sun aukawa garin Pissa dake ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja. Inda suke ci gaba da sanyawa garin wuta.

Wani mazauni garin ya shaidawa Gaskiya News Hausa cewar, su na cikin garin kwatsam s**a ji shigowar ÿàn̈ ťà'àđđa, wanda hakan yasa s**a nemi hanyar tsira da ransu. Ya ƙara da cewar zuwa yanzu babu abunda ido ke hangowa sai hayaƙin wutan da ÿàn̈ ťà'àđđan ke sanyawa garin.

Kawo izuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen garin da ýan̈ ťà'àđđan s**a kashe ba, da kuma irin girman hasara da ɓarnar da s**a yi a garin.

Ku sanya al'ummar wannan gari da sauran ƙauyukan yankin cikin addu’o’in ku.

12/06/2026

A wurinmu mahardacin Al-Qur'ani Mai Girma ko wanda ya sauke shi yafi professor muhimmanci.

10/06/2026

Abba Sani Pantami

10/06/2026

Sanar da sacewar waya 📱 ko babur 🏍️ a dandalin sada zumunta salon maula ne kawai. Madadin haka sai mutum ya ɗauki ƙaddara tare da fatan Allah Maida mishi mafi alkhairi kurum.

Address

Wuse Ll Abuja
Wuse II

Telephone

+2348029977786

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lokaci Baƙo Ne posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category