03/09/2026
Abu biyu masu ban tsoro akan makomar arewa;
----------------------------
1. Da tsakar rana na haɗu da wata matar aure, ta goyo yaro a bayan ta, da wasu yara guda biyu riƙe a dama da hagun ta
Zafin rana na dukan jikin matar, yaron dake goye a bayan ta sai kuka yakeyi, takalmin matar ya tsinke 🥹💔
Nace; Mama ina zuwa haka? Tace ɓarayi sun bada sanarwar shigowa, shine muka gudu zuwa cikin gari
Nace; Kina da 'yan uwa acikin gari ne? Tace a'a zata nemi guri ta ɓuya a gidan mai ko makaranta 🥹💔
= Wallahi sai da hawaye ya zubo a ido na.
Akwai irin wannan matar sunfi dubu hamsin dake gudun hijira da ƙananan yara a arewa, saboda matsalar tsaro.
Sauro, iskan damina, zafin rana, ruwan sama duk a kansu yake ƙarewa.
----------------------------
2. Wani abokina dake kasuwanci a jahar Lagos yake gayamin;
Matan hausawa dake gudun hijira a Lagos, mafiyawansu amfani akeyi dasu (zina) ana biyansu kuɗi domin su samu abinda zasu siye abinci da magani 🥹💔
Yara mata masu shekaru 13,14,15,16 duk an lalata su da iyayensu saboda su 'yan gudun hijira ne
A t**i ƙarƙashin gada ake zina da yaran mu domin a basu abinci 😭🥲
----------------------------
⚠️ Ku cire kwaɗayi da neman duniya ku zaɓi shugaba nagari wanda zai kawo mana tsaro
Idan bahaka ba, billahillazi abunda yake faruwa a yanzu fiye dashi zai faru zuwa gaba
Wannan matsalar tsaron da kuke gani, sai ta mamaye ƙauye da birni idan mukayi wasa.
⚠️ Ku daina ɗaukar siyasa amatsayin hanyar neman kuɗi da arziki
Ka tambaye kanka, shin menene makomar 'ya'yan da zaka haifa zuwa gaba??