15/10/2026
DAGA YOLA: Dubban Magoya Bayan Tinubu Sun Gudanar da Gangamin Neman Wa’adi na Biyu a 2027
Dubban magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun gudanar da gangamin neman sake zaɓensa a 2027 a birnin Yola, jihar Adamawa. Kodinetan ƙasa na ƙungiyar TMGA 2027, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya ce an shirya gangamin ne domin nuna goyon baya ga shugaban ƙasa da manufofin gyaran tattalin arzikinsa, yayin da Sakataren APC na jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, ya bayyana aniyar jam’iyyar na tattara magoya baya domin ganin Tinubu ya samu wa’adi na biyu.