17/07/2026
MU DAINA YAUDARAR KANMU... AKWAI TAZARA MAI NISA TSAKANIN ƊAN MASU KUƊI DA ƊAN TALAKA.
Zaka ga matashi ya fito daga gidan da ba a san tabbas ɗin abincin dare ba, amma yana gogayya da yaron da kansa yake a kwance a gidan da komai ya wadata. Wannan yaudarar kai ce babba.
Idan ka taso a gidan talakawa, rayuwarka ta sha bamban nesa ba kusa ba da wanda ya taso a gidan masu kuɗi. Su ƴaƴan attajirai, kusan komai nasu a shirye yake; abincinsu, sutura, kuɗin makaranta, gida, mota, aikin gwamnati, har ma da jarin kasuwanci an riga an tanadar musu da kadarorin gado. Suna yin rayuwa ne babu fargabar gobe.
Amma a matsayinka na wanda ya taso a gidan talakawa, ga wasu haƙiƙanin abubuwa guda biyar da ba za ka taɓa tsallake su ba, waɗanda ya zama dole ka cire wasa a ranka ka fita ka fuskance su da gaske:
1.
Nauyin Rayuwarka Da Karatunka: Kai ne za ka ɗauki nauyin karatun ka. Babu wanda zai riƙa aiko maka da maƙudan kuɗi. Kai ne za ka yi fafutuka ka nemi abincinka, suturarka, zirga-zirga, har ma da magani.
2.
Neman Aiki Ba Tare Da Connection Ba: Bayan ka kammala karatu da ƙyar da gumi, za ka shiga wata sabuwar rayuwar neman aiki tuƙuru. Ba ka da wani babban mutum da zai tsaya maka ya ba ka aiki a babban ofishi, don haka dole ka jure raini ka ci gaba da neman na kanka ba tare da karaya ba.
3.
Ƙirƙirar Jari Da Kasuwanci: Idan kuwa aikin gwamnati ya ƙi samuwa, ba za ka koma gida ka jingina da bango ba. Dole ne ka ka fita ka nemi jarin da za ka fara ƙaramar sana'a ko kasuwanci, komai ƙanƙantarsa, domin ka ceto rayuwarka da ta ahalinka daga halaka.
4. Dawainiyar Gina Rayuwa Da Aure: Kai ne za ka siyi fili ka gina gida, ko ka nemi kuɗin k**a haya mai kyau. Kai ne za ka nemi matar aure, ka ɗauki nauyin sadaki, lefe, bikin aure, sannan ka fara ɗaukar nauyin sabon iyalin da ka gina. Babu wata dukiya a ajiye da kake jira.
5. Zama Gatan Dangi: Bayan ka yi nasarar tsallake duk waɗannan ƙalubalen, dangi, iyaye, yayu da ƙanne za su dawo kanka. Kai ne za ka zama gatan su. Kai za ka ɗauki