Sirrin Girki

Sirrin Girki Alhamdulillah Masha Allah 😻

20/07/2025

GIVEAWAY GIVEAWAY GIVEAWAY
KUYI FOLLOWING DINA KU AJIYE SCREENSHOT DA PHONE NUMBER
KUYI SHEARING AND LIKE START ZUWA KARFE 5:30 ZAN GAMA
Maman Ikraam Muh'd
Maman Ikram muh'd zakuyi following faka faka Kati take sakawa

10/01/2025

With Mubashir Suleiman Gidan-hamma – I just got recognised as one of their top fans!

Oga Kamin like banga kudi ba 😔😔Itz senior
13/12/2024

Oga Kamin like banga kudi ba 😔😔
Itz senior

08/12/2024

With Itz Senior – I just got recognized as one of their top fans!

LEMUN KAYAYYAKIN LEMUN (FRUIT DRINK)Za’ayi amfani da duka kayan marmarin da muka yi amfani da su a sama.Za’a zuba a ciki...
24/11/2023

LEMUN KAYAYYAKIN LEMUN (FRUIT DRINK)

Za’ayi amfani da duka kayan marmarin da muka yi amfani da su a sama.

Za’a zuba a cikin blender a markada su.

Tace da rariya mai laushi (kara ruwa idan kina bukata).

Zuba suger yadda kakeso ( Idan kina da bukata zuba masa madara).

FURUT SALAD (FRUIT SALAD)Kayan hadi:-•Abarba•Gwanda•Ayaba•Kankana•Leman zaki•Kwakwa•Leman tsami•SugerYadda Ake Hadawa-Za...
24/11/2023

FURUT SALAD (FRUIT SALAD)
Kayan hadi:-

•Abarba
•Gwanda
•Ayaba
•Kankana
•Leman zaki
•Kwakwa
•Leman tsami
•Suger

Yadda Ake Hadawa

-Za’a yanka duk kayan marmarin kanana-kanana(cubes). Za’a bare leman zaki sala-sala sannan acire kwallon a zubar,a tara totuwar leman da ruwan leman a kofi.

Goga kwakwa kanana. Matse leman tsami a kwano,yanka ayaba kanana-kanana sai a zuba cikin leman tsami (yin haka yana hana ayabar tayi baki).

Dafa suger da ruwa ajiye gefe daya. Za’a hada duka yankakkun kayan marmarin waje daya acikin abun da ake hada fruit salad.zuba suger aciki juya sosai.

Idan za’a sha zaka iya zuba condensed milk akan fruits din.

24/11/2023

LEMUN KWAKWA DA ABARBA (PINACOLADO)
Kayan hadi:-

•Kwakwa
•Abarba ko leman zaki
•Suger
•Flavour na abarba

Yadda Ake Hadawa

-Za’a goga kwakwa da abun goga kubewa,markada a blender sai a zuba ruwan sanyi a tace da rariya.markada abarba ko [leman zaki] taceta zuba a kwano.dafa suger da ruwa barshi ya huce.

Hada kwakwa da abarba guri daya ko leman zaki zuba suger da flavour juya sosai asa a frig(Refrigerator) yayi sanyi.

wannan leman ana hadashi ne lokacin da za’a sha.idan kuma aka hada aka sa shi a frig(Refrigerator) za’a ga man kwakwar ya taso,ba lalace wa yayi ba sai akara markadawa.

24/11/2023

LEMUN SHAYI MAI SANYI (ICE TEA)
Kayan hadi:-

•Ganyan shayi
•Suger
•Leman tsami
•Na’a-na’a
•Kanunfari

Yadda Ake Hadawa

– Za’a dafa duka kayan amma banda suger da leman tsami.dafa suger da ruwa.matse leman tsami a kofi ajiye gefe daya.

Tace ganyan shayi da rariya, zuba suger da leman tsami. Saka cikin firijin(Refrigerator) yayi sanyi sosai.

Idan za’a sha saka ganyan na’a-na’a da aka tsinka guda biyar a ciki da leman tsamin da aka yanka akekkewayo a ciki.a kuma dauki slice daya a yanka bakinsa kadan a saka ajikin bakin kofin. Za’a sha da strew.

24/11/2023

LEMUN TSAMIYYA (TAMARIN JUICE)
Kayan hadi:-

•Tsamiya
•Suger
•Kanunfari
•Citta
•leman tsami

Yadda Ake Hadawa

– Dafa suger da ruwa barshi ya huce.dafa tsamiya da ruwa,kanunfari da citta har misalin minti 30.tace tsamiyar abarshi ya huce yayi sanyi.

Matse leman tsami a kuma yanka guda biyu yankan fadi.hada dafaffan suger acikin tsamiya zuba leman tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.asaka cikin frig(Refrigerator) yayi sanyi sosai kafin sha.zaka zuba ruwa dai dai tsamin da kakeso kafin sha.

LEMUN KARYA KUMALLO (BREAK FAST NOG)Kayan hadi:-•Madara•leman zaki•yoghurt•nutmeg•ayaba•sugerYadda Ake Hadawa– Zuba lema...
24/11/2023

LEMUN KARYA KUMALLO (BREAK FAST NOG)
Kayan hadi:-

•Madara
•leman zaki
•yoghurt
•nutmeg
•ayaba
•suger

Yadda Ake Hadawa
– Zuba leman zaki,ayaba,madara da yoghurt a cikin blender idan sun markadu sosai juye a jug,za’a sa a frig(Refrigerator) ko a zuba kankara,zuba nutmeg akai idan kanaso.

LEMUN ABARBA DA NONO (PINEAPPLE AND YOGURT ICE)Kayan hadi:-•Abarba•Yoghurt•Flavor•Suger Yadda Ake Hadawa-Yanka abarba ma...
24/11/2023

LEMUN ABARBA DA NONO (PINEAPPLE AND YOGURT ICE)
Kayan hadi:-

•Abarba
•Yoghurt
•Flavor
•Suger



Yadda Ake Hadawa

-Yanka abarba markada a blender,tace zuba a kwano,zuba yoghurt akai da flavour,suger da kuma kankara,za’a sha da sanyi.

Address

Gombe

Telephone

+2349161101823

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sirrin Girki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sirrin Girki:

Share

Category