Rayuwa da Sunnah

Rayuwa da Sunnah DOMIN YAƊA ILMIN ADDININ MUSULUNCI
(2)

13/08/2026

Assalamu alaikum warahmalullah wa barakãtuh, In shã Allah shafin da Sunnah zai cigaba da kawo karatuttukan malaman Sunnah

05/08/2026

Subhanallah 😥

16/07/2026
KAƊAN DAGA CIKIN SIFFOFIN AHLUSSUNNAH WAL-JAMÃ'AH-----------------------------------Ahlus-Sunnah wal-Jamā'ah su ne waɗan...
11/07/2026

KAƊAN DAGA CIKIN SIFFOFIN AHLUSSUNNAH WAL-JAMÃ'AH
-----------------------------------
Ahlus-Sunnah wal-Jamā'ah su ne waɗanda ko da yaushe suke ƙoƙarin bin Al-Qur'ani da ingantacciyar Sunnah bisa fahimtar Sahabban Annabi ﷺ da magabatan ƙwarai (Salaf).

Kuma Malamai magabãtã sun bayyana wasu siffofi da suke nuna cewa mutum AhlusSunnah neh daga ciki akwai,

1. Riƙo da Al-Qur'ani da Sunnah a matsayin tushen addini.
Fahimtar addini bisa tafarkin Sahabbai da Tabi'ai.

2. Tauhidi tsantsa, ba tare da haɗa wani da Allah cikin ibada ba.

3. Bin Sunnar Annabi ﷺ da nisantar bidi'o'in da s**a saɓa da koyarwarsa.

4. Girmama Sahabbai gaba ɗaya, tare da guje wa zagi ko ƙyama gare su.

5. Kiran mutane zuwa alheri, da umurni da kyakkyawa da hani daga mummuna cikin hikima.

6. Tsayawa a kan gaskiya, ko da suna fuskantar ƙalubale.

7. Haɗin kai tsakanin Musulmi, tare da guje wa rarrabuwar kawuna da fitintinu.

8. Haɗa ilimi da aiki, ba ilimi kaɗai ba.

Allah Maɗaukaki Ya ce:
"Idan kun yi jayayya a kan wani abu, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa." (Suratun An-Nisā'i: 59)
Kuma Annabi ﷺ ya ce:
"Na bar muku abubuwa biyu; idan kuka riƙe su ba za ku ɓace ba: Littafin Allah da Sunnata." (Hadisin yana da hanyoyin ruwaya da malamai s**a tattauna game da ingancinsa.)

Waɗannan kaɗan ne daga cikin siffofin AhlusSunnah Wal-Jamã'ah

08/07/2026

kar mu manta da Azkãr ɗin yamma

Address

Kano
Gwarzo

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rayuwa da Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share