11/08/2026
HANYOYIN GASAWA ƊAN BIDI'AH AYA ATAFIN HANNU 😋 (Part 10)
“Idan kace Annabi ﷺ yayi, ka kawo mana hujjar data tabbata.
A addini, ba wai duk abin da aka jingina wa Annabi ﷺ ne yake zama hadisi ba. Sai an tabbatar da ingancinsa.”
Ku tambaye shi:
Ina wannan hadisin yake?
Wane Sahabine ya rawaito shi?
Wane malamin hadisi ya inganta shi?
Idan ya kawo hadisi mai rauni ko wanda ba a san asalinsa ba, kada kuyi gaggawar karba. Kuce:
Shin wannan hadisin ya isa ya kafa sabuwar ibada?
Annabi ﷺ yayi gargadi:
«مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ»
Ma'ana:
Duk wanda yayi mini karya da gangan, toya tanadi mazauninsa a cikin wuta.
Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim.
Ku Tuna!
Jingina magana ga Manzon Allaah ﷺ al'amari ne mai girma. Baza muce “Annabi ya ce” basai mun tabbatar.
Addininmu yafi darajar mu kare shi da magana marar tushe. Idan ka kasa tabbatar da hadisin, ka tsaya; domin tsayawa a kan abin da baka sani ba shine tsira.
Ya Allaah Yasa mu zama masu fadin gaskiya a kan ManzonSa ﷺ, kuma Ya kiyaye mu daga jingina masa abin da bai fada ba. Ameen.
KUYI FALLOW, LIKE, SHARE, NAGODE