14/08/2026
Atiku Ya Maka Tinubu Kotu Kan Takardar NYSC, Ya Nemi Hana Shi Takara a 2027.
DH Hausa TV
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin kalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu shiga zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
A cikin ƙarar, Atiku da jam’iyyar ADC sun yi zargin cewa an gabatar wa INEC da takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC mai ɗauke da sunan bTinubu Bola Adekunle, maimakon sunan Bola Ahmed Tinubu.
NMasu ƙarar sun nemi kotu ta binciki sahihancin takardar, tare da umartar INEC ta gabatar da Form CF001 da Tinubu ya gabatar dangane da zaɓen 2023 da na 2027.
Atiku da ADC sun dogara da tanadin Sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya shafi rashin cancantar mutumin da aka tabbatar ya gabatar da takardar shaidar bogi ga INEC.
Sun kuma nemi kotu ta hana Tinubu da jam’iyyar APC shiga zaɓen 2027 idan har aka tabbatar da zarge-zargen da s**a gabatar.
Atiku ya jaddada cewa manufar ƙarar ita ce a bai wa kotu damar duba hujjoji da takardu domin yanke hukunci bisa doka, maimakon a yanke hukunci ta kafafen sada zumunta.
Ya kuma bukaci INEC da ta gabatar da takardun da ake nema domin tabbatar da gaskiyar lamarin, yana mai cewa babu wani ɗan Najeriya da ya fi ƙarfin Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.
DH Hausa TV