28/07/2025
Cushewar Kasuwar Burola Ze Tilasta Raba Kafa A Kasuwar Zabo.
Yadda Ghanaian s**a bawa kiwon zabi muhimmanci ba haka abun yake a Nigeria.
Ko a kudancin Najeriya Babu gidajen gona da yawa iya na zabi zalla.
A Ghana ne zaka samu gidan gona mai dauke da zabi zalla sama da zabo 10,000. Ban da kananan gidaje masu 5000, 4000, 3000.
Lissafin nan fa na zabi bayan ya zama mature a fili yake, Kuma kusan kowa ma ya sani.
Yanzu fa dabarar da ake wa zabi shi ne da zarar sun gama kwai a October-November zuwa January sun ci ciyawa zasu cigaba da wani kwan. So, all year round yanzu ake samar da zabo.
Ka taba ganin kwayayen zabi lokacin azumi? Ka taba ganin kwayayen zabi da rani sosai?
A na ta cigaba fa.
Na ce ko ba za ka ware gidan gona musamman na zabi ba, mai zai hana ka zubasu a farfajiyar gidan gonarka? Sai ya zama wata ribar kafa gareka! A ce akwai zabi kamar dubu uku ma a farfajiyar gidan gonarka suna yawo suna cin ciyawa da Kwari da sauransu. Da safe ka Watsa musu tsaba, da yamma ma ka Watsa musu.
Ai idan lokacin fitar da su ya yi na tabbata sai ka godewa Allah.