Dr Ayman muhd Sareena

Dr Ayman muhd Sareena Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dr Ayman muhd Sareena, Grocers, Kano State Nigeria � Garko local Government Sareena, Kano.

Farashin dizal a kasar Amurka ya kai sabon matsayi mafi girma a tarihi, inda lita 3.9, wato galan guda, ta kai dala 5.85...
07/09/2026

Farashin dizal a kasar Amurka ya kai sabon matsayi mafi girma a tarihi, inda lita 3.9, wato galan guda, ta kai dala 5.85, sakamakon tasirin yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.

Bayanan ƙungiyar masu ababen hawa ta Amurka, AAA, sun nuna cewa sabon farashin ya zarce tsohon tarihi da aka samu a watan Yunin 2022 bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Farashin dizal na iya ƙara tsadar sufuri da samar da kayayyaki, musamman saboda ana amfani da shi wajen sarrafa manyan motoci, motocin haya, jiragen ƙasa da manyan injuna.

Haka kuma, farashin fetur ya kai dala 4.14 kan galan guda, wanda shi ma ya zama mafi tsada da aka taɓa samu a wannan lokaci, gabanin hutun ranar Ma’aikata a Amurka.

Ƙungiyar AAA ta ce rikicin da ke ci gaba da faruwa a mashigar Hormuz ya sanya farashin ɗanyen mai ya kasance a kusa da dala 90 kan ganga guda.

07/09/2026

Amfani 30 nayin sadaka duniya da Lahira duba comment section 👇👇

06/09/2026

🌙⚠️ ABUBUWA 7 DA YA KAMATA KA NISANTA DA SU KAFIN KA KWANCI YA BACCI 👇👇

YADDA AKE WANKAN JANABA 👇🏻Ka yi niyya a zuciyarka cewa: Na yi niyyar yin wankan janaba domin neman tsarki don yin ibada....
06/09/2026

YADDA AKE WANKAN JANABA 👇🏻

Ka yi niyya a zuciyarka cewa: Na yi niyyar yin wankan janaba domin neman tsarki don yin ibada. Ba dole sai ka furta niyyar da baki ba.

Ka wanke hannuwanka, sannan ka wanke duk wata najasa da ke jikinka.

Ka yi alwala kamar yadda ake yi kafin sallah.

Ka zuba ruwa a kai har ya kai asalin gashin kai, ka tabbatar fatar kai ta jike.

Ka zuba ruwa a dukkan jikinka, ka tabbatar ruwa ya isa ko’ina karkashin hamata, cibiya, tsakanin yatsu, bayan kunnuwa da sauran wuraren da ruwa zai iya kasa kaiwa.

Kada ka yi almubazzaranci da ruwa. Ba a kayyade wani adadin lita na ruwa da dole sai an yi amfani da shi ba. abin da ake bukata shi ne ruwa ya game jiki gaba daya.

Babu wata addu’a ta musamman da aka tabbatar da za a furta lokacin fara wankan janaba. Muhimmin abu shi ne niyya a zuciya da tabbatar da ruwa ya game jiki gabadaya.

Wallahu A‘lam.

Fly Geyser A jihar Nevada A Kasar Amurka A haka Allah Ya Hallici Wannan Dutsen Da Yake Fesar Da Ruwa. Fly Geyser yana ka...
06/09/2026

Fly Geyser A jihar Nevada A Kasar Amurka

A haka Allah Ya Hallici Wannan Dutsen Da Yake Fesar Da Ruwa. Fly Geyser yana kan Fly Ranch, yanki mai girman eka 3,800 a Arewacin Nevada a kasar Amurka, wanda Burning Man Project ya siyi wajen a cikin 2016. Wannan Waje Yana Ban Al'ajabi. Ruwan ya na da zafi sosai, ba za a iya amfani da shi don ayyukan noma ba. Yanayin zafin ruwan da ke fitowa daga Dutsen zai iya wuce 200 °F (93 °C).

‎Lahaula walaquwwata illah billah 🤔 ✊.‎Malam ƙasar Russia duniya ce mai zaman kanta a duniyar kimiyyar makaman azaba. Wa...
05/09/2026

‎Lahaula walaquwwata illah billah 🤔 ✊.
‎Malam ƙasar Russia duniya ce mai zaman kanta a duniyar kimiyyar makaman azaba. Wannan makamin da kuke gani sunan sa "Avangard Hypersonic Messile". Yanzu haka shine makami mai linzamin da yafi kowanne irin makami gudu a kaf faɗin duniya. Kafin Russia ta ƙirƙiri wannan makamin, ƙasar America ce take da makamin "Tomahawk" wanda shine Hypersonic Land Messile mafi gudu wanda yake cikin tazarar 920 km per hour. Yanzu da ƙasar Russia ta ƙirƙiro wannan Avangard Hypersonic Messile ɗin, gudun sa ya ninka gudun Tomahawk sau 31. Tomahawk yana gudun 920km/h, a yayin da Avangard Hypersonic Messile yake gudu 32,200km/h. Malam idan baka gane ba, wurin da Tomahawk zai je a cikin minti 81, wannan Avangard Hypersonic Messile ɗin cikin minti 2 zai je wurin. Google it idan kana kokwanto.👌

‎Cikin awa ɗaya daga Maiduguri zai je Lagos ya dawo sau goma 16. Idan kana ƙofar Dawanau, tun kafin ka ƙaraso rijiyar lemo ko ƙofar Ruwa wannan makamin tuntuni ma ya fice daga Nahiyar Africa. Magana ce ake ta gudun lahaula walaquwwata illah billah. Wannan makamin na Avangard Hypersonic, ƙasar Russia ta ƙera shi ne a matsayin Intercontinental Ballistic Messile. Kalar ƙirar da s**a yi masa already daman sun yi shine saboda ya huda nahiya baki ɗayan ta saboda jan kunnen masu shegen kunnen ƙashi. Ko B2 Bomber Spirit ɗin da ƙasar America take ta zuzutawa duk ƙarya ce gudun kilomita 1000 ce yake yi a cikin awa ɗaya👌. Wannan makamin na Avangard Hypersonic Messile shine makamin da ƙasar Iran take ta ƙoƙarin ganin Russia ta basu shi amma har yanzu Putin bai basu ba saboda ya san cewa tabbas idan IRGC su ka mallaki wannan makamin ina rantse muku da Allah sai sun harba shi Pentagon ko tsakiyar birnin Tel Aviv. Shi kansa Putin ɗin ya san wannan shiyasa ya hana su. Saboda haka 'yan Nigeria ku cigaba da zaɓar APC da karnukan cikin ta. Ku da ganin cigaba saidai a TV ko a gidan jarida believe me👌

05/09/2026

AKWAI SIHIRI A JIKIN KA, IN HAR KANA YIN WANNAN MAFARKAI GUDA HUDU (4) 👇👇

ABUBUWAN 5 DA KE IYA SA MUTUM YA YI ASARAR RAYUWARS A DUNIYA DA LAHIRA! Ka tsaya ka karanta wannan. Wasu abubuwa ba sa k...
05/09/2026

ABUBUWAN 5 DA KE IYA SA MUTUM YA YI ASARAR RAYUWARS A DUNIYA DA LAHIRA!

Ka tsaya ka karanta wannan. Wasu abubuwa ba sa kashe mutum nan take amma suna iya lalata rayuwarsa a hankali—su rage masa albarka su bata dangantaka da mutane kuma su nisanta shi daga abin da ya dace.

Ga abubuwa 5 da ya kamata ka yi hattara da su:
❶ BARIN SALLAH DA IBADA
Idan mutum ya fara sakaci da ibadarsa zuciyarsa na iya yin nisa da Allah ba tare da ya lura ba. Kada ka bari neman duniya ya sa ka manta da wanda Ya ba ka duniya.

❷ CIN HAKKIN MUTANE
Dukiya ko matsayi ba su sa zalunci ya zama halal ba. Ka kiyaye hakkin mutane domin abin da mutum ya ci ba bisa gaskiya ba na iya zama babban nauyi a kansa.

❸ BIN SON ZUCIYA BA TARE DA HANKALI BA
Ba duk abin da zuciya take so ne yake da amfani ba. Wani lokaci abin da kake ganin zai faranta maka rai yau shi ne zai iya zama nadama gobe.

❹ MANTAWA DA MUTUWA
Rayuwa tana iya yaudarar mutum ya ji kamar zai kasance a duniya har abada. Amma gaskiyar ita ce, kowa yana da lokacin da zai bar duniya. Don haka ka yi amfani da lokacin da Allah Ya ba ka kafin lokaci ya kure.

❺ DOGARO DA DUNIYA KAWAI
Kuɗi abokai matsayi da suna duk abubuwa ne masu iya canzawa. Ka nemi abin duniya amma kada ka bari duniya ta zama ita kaɗai burinka. Ka gina rayuwarka da abin da zai amfane ka a duniya da lahira.

GASKIYAR DA YA KAMATA KA TUNA:
Mutum zai iya tara dukiya ya samu suna ya samu abokai da matsayi… amma idan ya rasa kyakkyawar zuciya gaskiya da tsoron Allah akwai abin da ya rasa wanda kuɗi ba za su iya saya masa ba.

Kada ka jira wata rana ta zo da za ka ce: “Da ace na gyara tun da wuri…
Ka fara gyara kanka tun yau.

ALLAH YA SA MU ZAMA DAGA CIKIN WAƊANDA SUKE GYARA KANSU KAFIN LOKACI YA KURE.

Prince Ilah Bn Umar ✍️

Malam Usman Maidubun Isa ya bayyana cewa nan gaba kaɗan zai daina yin yabon Annabi Muhammad (S.A.W.) tare da amfani da k...
05/09/2026

Malam Usman Maidubun Isa ya bayyana cewa nan gaba kaɗan zai daina yin yabon Annabi Muhammad (S.A.W.) tare da amfani da kiɗa, yana mai cewa a halin yanzu yana yin hakan ne bisa abin da ya kira “lalura.”

Malam Usman ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yadda yake gudanar da yabon Annabi (S.A.W.), inda ya nuna cewa akwai yiwuwar ya sauya salon yabon nasa a nan gaba.

Ya kuma ce a halin yanzu yana ci gaba da yin yabon ne tare da kiɗa saboda lalurar da yake ciki, yayin da yake hasashen cewa nan gaba kaɗan zai daina amfani da wannan salon.

Shin Maizakuce..?

Ko Ba Mutuwa Akwai Tsufa!Baƙar mace ta farko da ta fara aiki a kamfanin kayan ado "Ford Agency" na ƙasar America Ɓaƙar m...
05/09/2026

Ko Ba Mutuwa Akwai Tsufa!

Baƙar mace ta farko da ta fara aiki a kamfanin kayan ado "Ford Agency" na ƙasar America

Ɓaƙar mace ta farko da aka fara wallafawa a mujallar "Harper’s Bazaar"

Saboda kyan fuskar ta da kyan jikin ta, aka ware mata shafuka na musamman acikin mujallar "American Vogue"

Ta kammala karatun digirin shari’a a Jami’ar Cambridge University

Tayi "Call to Bar" a Ingila

Tayi zama ministan harkokin ƙasashen waje

Tayi zama a ofishin jakadancin America

Ta auri wani ƙwararren injiniyan jiragen sama a ƙasar London, kuma yariman gidan sarauta "Wilberforce Nyabongo"

Yanzu ta tsufa sosai (90 years) +

Kyan fuskarta ya gushe

Dirin jikinta ya zube

Gashin kanta yayi fari

Fatar jikinta ya tsuke

Haƙoranta sun zube

Bata riƙe da kowane irin muƙami

Ta dawo gida a ƙasar Uganda da zama

Duniya ɗauka take tana ajiyewa

Yau idan kaine a sama, gobe zaka sauka wani ne zai hau

Duk wanda duniya ta hanashi bin Allah da tsoron Allah, shine cikakken asararre.

Coped

Address

Kano State Nigeria � Garko Local Government Sareena
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Ayman muhd Sareena posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category