16/06/2026
JIYA BA YAU BA: Ali Kwara Jarumin Dazuka Na Arewa
Ali Kwara ba shi da uniform, amma sunansa ya kasance abin tsoro ga miyagu.
Ali Kwara, wanda aka fi sani da Alhaji Ali Muhammad Kwara, fitaccen ɗan Bauchi ne daga garin Azare a ƙaramar hukumar Katagum. Ya shahara a Arewacin Najeriya saboda jarumtar sa wajen yaƙi da ‘yan fashi, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
A rayuwarsa, Ali Kwara ya kasance ɗan farauta hunter mai haɗin gwiwa da jami’an tsaro k**ar ‘yan sanda da sojoji wajen bin sahun miyagun mutane a cikin dazuka. A lokuta da dama, ya jagoranci hare-hare tare da taimaka wa gwamnati wajen k**a manyan laifuffuka da kwato mak**ai daga hannun ‘yan ta’adda.
Ya yi fice musamman a jihohin Arewa k**ar Bauchi, Gombe, Katsina, Zamfara da wasu wurare, inda yake shiga dazuka yana bin sawun ‘yan bindiga domin ya tarwatsa su ko a k**a su. Wannan jarumta ta sa mutane da dama s**a fara kiransa da “Jarumin Dazuka” ko “Thief Catcher.
Ali kwara ya yi kusan shekaru 20+ yana aiki tare da hukumomin tsaro, yana taimakawa wajen gano miyagun mutane da kuma mika su ga ‘yan sanda domin shari’a. Duk da haka, bai kasance jami’in gwamnati kai tsaye ba, amma ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaki da rashin tsaro.
Ali Kwara ba kawai jarumi ba ne a fagen yaki da laifi, har ila yau mutum ne mai taimako. A garin sa na Azare, yana ciyar da marasa galihu, yana tallafa wa marayu da zawarawa, har ma yana taimaka wa iyalai da mabukata ba tare da wata tambaya ba.
Tsawon shekaru da dama, ya shiga dazuka yana bin sawun miyagu, yana taimakawa jami'an tsaro wajen k**a masu laifi da kwato mak**ai.
Ba jarumi kawai ba ne, ya kasance mai taimakon marasa galihu, marayu da zawarawa a cikin al'ummarsa.
Wani abin ban sha’awa shi ne yadda aka rika cewa da zarar ‘yan ta’adda sun ji sunansa a yankin da suke, sai su tsere ko su wargaje, saboda tsoron sa da jarumtar sa.
A ƙarshe, ya hadu da iftila’in rashin lafiya har ya rasu a ranar 6 ga Nuwamba, 2020 a Abuja bayan fama da jinya.