26/06/2026
Verydarkblackman vs Arewa
Muna ta zagin Verydarkman saboda ya faɗa mana gaskiyar da ba ma son ji, amma har yau mun kasa ƙaryata waɗannan alƙaluman da hujjoji na zahiri:
Mu ne muke da ƙungiyar masu garkuwa da mutane a ƙasar nan.
Mu ne muke da ta ƴan ƙunar baƙin wake da masu tayar da kafatanin gari a ƙasar nan.
Mu ne muke da ƴan Boko Hrm da duka ragowar ƙungiyoyin ƴan ta'*dda masu iƙirarin jihadi.
Kaso 70 zuwa sama na mabaratan ƙasar nan duk namu ne.
Mu ne muka fi kowa yawan haihuwa barkatai da walaƙantar da yaranmu akan t**i.
Za mu iya shafe tsawon shekaru ba mu iya yi wa azzaluman shugabanninmu ko da zanga-zangar lumana ba, amma a cikin daƙiƙu za mu iya k*she malamar islamiyya talaka bisa zargin da ba mu da tabbaci.
Za mu iya k*she ɓarawon waya, mu ɗora masa taya a kansa, mu cinna masa wuta amma shugaban da ya sace tiriliyan 210 mu mayar da shi waliyyi har mu dinga gadinsa da rayuwarmu.
Yau kusan kaso 90 na ta'addancin da ake yi a Najeriya a Arewa ake yin sa, amma ko a gobe aka ajiye mana akwatun zaɓe a Arewa, APC ce za ta cinye.
A yau a iya Arewa kawai an tashi garuruwa kimanin 3,000, amma a cikin waɗannan mutanen da s**a rasa muhallansu, rayukan ƴaƴansu da ƴan’uwansu sai ka sami kaso mai yawa da suke tallata APC.
Ga shi mu muka fi kowa gauraya gargajiya da addini shi ya sa yau bara har ta bar iya kan yara almajirai ta tafi kan matan aure da maza magidanta majiya ƙarfi.
Mu ne muke naɗawa kuma mu muke sauke shugaban ƙasa a Najeriya amma har yau babu walaƙantattu a wurin ƴan siyasa a Najeriya kamar mu, don har yau ₦500 da Klin da taliya na iya siyen ƙuri’armu.
Har yau a Arewa za a iya sacewa kuma a kashe mana mutane masu tarin yawa amma a ranar, Salim Goje ko Hadiza Gabon za su iya zama mana abin da muka fi tattaunawa a kafar sadarwarwa.
Mun ƙasa faɗa wa kanmu gaskiya, kuma mun hana kowa ya faɗa mana, sannan a hakan jira muke mu ga sauyi ya faɗo mana daga sama.
An gaya mana matsalolinmu amma muna maganar Ɗangote da BUA wai ƴan Arewa ne — amma mun manta