Masarautar Kaura Namoda

Masarautar Kaura Namoda From kaura namoda Emirate council

Honoured to witness the participation of His Royal Highness, Major Dr. Sanusi Mohammed Ahmad Asha, FCNA, and his entoura...
13/07/2026

Honoured to witness the participation of His Royal Highness, Major Dr. Sanusi Mohammed Ahmad Asha, FCNA, and his entourage serving as the Representative of Traditional Rulers in Nigeria, at the National Validation and Adoption of the Standard Operating Procedures (SOPs) for the National Policy and Strategy on Disarmament, Demobilization, and Reintegration (DDR).

The high-level event is helding at the National Counter Terrorism Centre (NCTC), Office of the National Security Adviser (ONSA), Three Arms Zone, Abuja, underscoring the vital role of traditional institutions in promoting peace, security, conflict resolution, and national stability. Their inclusion reflects a shared commitment to strengthening community engagement and supporting sustainable peacebuilding across Nigeria.

03/07/2026

Daga Garin Sokoto, Mai Martaba Sarkin kiyawa kaura Namoda major Dr Sanusi Mohammed Ahmed Asha FCNA Tareda Mai Martaba Sarkin Dutse HRH Hamim Nuhu Sanusi.Allah yakara maku nasara,Amin 🤲

"Sarki Kakanka yayi,  Sarki Tsofonka yayi,  Tau kai ko kayi Sarki,  Gidan Basharun   Ummaru sun sani,   Koda baka nan su...
28/06/2026

"Sarki Kakanka yayi,
Sarki Tsofonka yayi,
Tau kai ko kayi Sarki,
Gidan Basharun
Ummaru sun sani,
Koda baka nan su
kayin Sarki".

Cewar Makaɗa Alh. (Dr.) Ibrahim Narambaɗa Tubali☝️ a wata waƙar babban ubangidansa, Sarkin Gobir na Isa Marigayi Malam Ahmadu Basharu (Ahmadu Bawa/Ahmadu I) mai amshi "Amadun Bubakar gwarzon Yari, Dodo na Alkali".

26/06/2026

Mai martaba sarkin kiyawan Kaura Namoda Major Dr sanusi Mohammed Ahmed Asha FCNA (Hadimul Qur’an) ya jagoranci Bude Masallacin Juma'a a jihar Sokoto.

A bisa Gayyatar Mai Darajar Gomnan jihar Sokoto Dr Ahmad Aliyu, Mai martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda ya Jagoranci bude wani katafaren Masallacin Juma'a a Garin Gada, Karamar hukumar mulkin ta Sokoto Wanda mai Daraja Gwamna Dr Ahmad Aliyu ya gidanawa al'ummar Garin Gada.

Sarkin Kiyawa Maj. Dr. Sanusi Mohammed Ahmad Asha shine babban bako na musamman kuma wanda ya bude wannan masallacin a yau juma’a 26/6/26

Muna yiwa Mai Martaba fatan Alkhairi da Rokon Allah shi karawa mai martaba Lafiya da Imani Amin

Daga fadar mai martaba sarkin kiyawan kaura namoda. inda mai Martaba sarkin kiyawan kaura namoda Major Dr Sanusi Muhamma...
03/06/2026

Daga fadar mai martaba sarkin kiyawan kaura namoda.

inda mai Martaba sarkin kiyawan kaura namoda Major Dr Sanusi Muhammad Ahmad asha mphil ya sanya Albarka ga mashin da Daya daga cikin Hadiman sa s**a samu daga mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mani malam mummuni.

SUKUWAR DAWAKI DA RAKUMADAY 5BUKIN SALLAH NA MASARAUTAR KAURA NAMODA, ZAMFARA STATE, NIGERIADa izinin Allah Gobe Mukadda...
30/05/2026

SUKUWAR DAWAKI DA RAKUMA
DAY 5

BUKIN SALLAH NA MASARAUTAR KAURA NAMODA, ZAMFARA STATE, NIGERIA

Da izinin Allah Gobe Mukaddashin GWAMNAN JIHAR ZAMFARA H E Mani Malam Mummuni ne zai kasan ce babban Bako a Wurin SUKUWAR DAWAKI DA RAKUMMA da za a yi Gobe Lahadi da misalin Karfe 4:30pm a filin Stadium kusa ga GSS Kaura.

Sukuwar wani bangare ne na bukukuwan HAWAN SALLAH BABBA da Masarautar Kaura Namoda ta shirya karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Maj. Dr. Sanusi Mohammed Ahmad Asha (Rtd) FSS, RMS psc, FCNA.

Allah ya bada ikon zuwa ameen.

Abdulrazak Bello Kaura
Development Journalist

Hawan sarki
29/05/2026

Hawan sarki

HAWAN BABBAR SALLAH EID AL-ADHA 2026/1447AH A MASARAUTAR KAURA NAMODAASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHSANARWA TA MUSAMMAN D...
24/05/2026

HAWAN BABBAR SALLAH EID AL-ADHA 2026/1447AH A MASARAUTAR KAURA NAMODA

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH

SANARWA TA MUSAMMAN DAGA MASARAUTAR KAURA NAMODA DAKE JIHAR ZAMFARA NIGERIA

Amadadin Maimartaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda HRH Major Dr. Sanusi Mohammed Ahmad Asha (Rtd) FCNA, ya umurceni da in gayyaci dukkan Al’ummar Masarautar Kaura Namoda da kewaye da kuma dukkan Al’ummar Jahar Zamfara da Kasa baki daya zuwa wajen Gagarumin Bukin Babbar Sallah wato Eid al-Adha 2026/1447AH na Masarautar Kaura Namoda wanda ta saba yi duk shekara, a bana za a fara bukin ne tun daga ranar Laraba 27 May, 2026 zuwa Lahadi 31 May, 2026 Insha Allah. Za’a gudanar da Bukin kamar haka:

RANA TA FARKO: HAWAN SALLAH

Rana: Laraba 27/5/2026
Wuri: Fadar Maimartaba Sarkin Kiyawa
Lokaci: 7:30AM

RANA TA BIYU: HAWAN SARKI

Rana: Alhamis 28/5/2026
Wuri: Daga Gidan Maimartaba Sarkin Kiyawa zuwa Fada
Lokaci: 4:30PM

RANA TA UKU: WASANNIN AL’ADUNMU

Rana: Jumu’a 29/5/2026 Wasan Al’adu, Wasan Jan Igiya, Wasan Langa, Wasan Kwaikwayo, Dabin Gogarma, Baja kolin masu maganin gargajiya, Harbin Kwari da Baka da sauransu.
Wuri: Kaura Namoda Stadium
Lokaci: 4:30PM

RANA TA HUDU: HAWAN DABA

Rana: Assabar 30/5/2026
Wuri: Fadar Mai Martaba Sarkin Kiyawa
Lokaci: 10:00AM

RANA TA BIYAR: SUKUWA WATO TSEREN DAWAKI DA RAKUMMA

Rana: Lahadi 31/5/2026
Wuri: Kaura Namoda Stadium
Lokaci : 4:30PM

Allah yabada ikon zuwa ayi buki lafiya kuma a kare lafiya amin.

Sanarwa daga Alh. Salisu Abubakar Magatakardan Kaura Namoda. Sakataren Masarautar
Kaura Namoda
Jihar Zamfara.
23/5/2026.

Alhamdulillah!Yau Laraba 06/05/2026 ne Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Dr. Sanusi Muhammad Ahmad Asha yake cika ...
06/05/2026

Alhamdulillah!

Yau Laraba 06/05/2026 ne Mai Martaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Dr. Sanusi Muhammad Ahmad Asha yake cika shekaru 6 kan karagar mulkin masarautar Kaura Namoda.

Muna rokon Allah ya ƙarawa Sarki lafiya da nisan ƙwana.

Allah yayi riko da hannayensa.

Address

Kaura Namoda Emirate Palace
Kaura-Namoda

Telephone

+2347030151385

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masarautar Kaura Namoda posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Masarautar Kaura Namoda:

Shortcuts

Share

Category