Hassan IBN- Salisu

Hassan IBN- Salisu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hassan IBN- Salisu, Grocers, Unguwan sarkin dokanlere, Lere.

09/08/2026

Me yasa aka raina Degree a ƙasar nan??

Shi dai Degree shaida ce ta wani mataki na ilimi, kuma ilimi abu ne mai daraja a ko’ina a duniya. Amma abin tambaya shi ne: me ya sa idan an yi magana kaɗan, sai ka ga wasu mutane suna kushe Degree, har da waɗanda su kansu s**a yi Degree?

A iya fahimtata, Degree ba shi da laifi; laifin wani ne ya shafe shi. Domin a asali, muhawarar da ake yi ita ce tsakanin entrepreneurs da employees; wato masu sana’a ko kasuwanci na kansu, da kuma waɗanda suke aiki a ƙarƙashin gwamnati, kamfanoni ko hukumomi. Laifin Degree guda ɗaya shi ne ya ƙyanƙyashe galibin employees. Wannan ya sa idan wasu entrepreneurs suke son kawo wa employees hari, sai su haɗa da Degree, wanda bai ji ba bai gani ba. Don haka, idan ana maganar adalci, babu ruwan Degree da wannan dambarwar.

Sannan ba duk entrepreneurs ne suke kawo hari kan Degree ba. Wani ɓangare ne daga cikinsu kawai, waɗanda a zahiri za a iya kiran su materialists; wato irin mutanen da suke fifita martabar kuɗi fiye da komai a rayuwa, har ma da ilimi. A wurinsu, duk wani abu da ba zai kawo kuɗi ba, to ɓata lokaci ne da wahala.

Irin wannan tunanin ne ma yake ƙara mamaye al’ummomin duniya a yau. Kowa ya birkice, an tashi hankalin mutane, an kuma tsoratar da su da talauci, har mutane da yawa s**a fara ganin kuɗi a matsayin shi kaɗai ne tudun tsira a rayuwa.

Ita kuma rayuwa, kowa akwai layin da ya ɗauka. Akwai mutanen da kuɗi ba shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwarsu ba. Domin mutane da dama suna yin Degree ba wai don su nemi kuɗi da shi ba, sai don neman ilimi, cika wani buri, ko cimma wani haƙiƙanin manufa da s**a sanya wa kansu a rayuwa.

Amma materialists suna kallon al’amura ne ta fuskar kuɗi kawai. A wurinsu, duk wani abu da ba zai kawo kuɗi ba, to shirme ne. Saboda haka, za su iya aibata abin da ya fi Degree daraja ma, matuƙar ba ya samar da kuɗi.

A ƙarshe, entrepreneurs da employees, kowa akwai inda Allah Ya sanya masa hanyar neman abincinsa a wannan duniya. Kuma a zahiri, rayuwa ba za ta daidaita ba sai da ɓangarorin biyu. Wani employee ne, domin wannan shi ne abin da ya iya kuma yake jin daɗin rayuwarsa a cikinsa; wani kuma entrepreneur ne, domin wannan shi ne hanyar da Allah Ya buɗe masa.

Ba dole ba ne mutum ya raina hanyar wani saboda kawai hanyar rayuwarsa ta bambanta da tasa. Darajar mutum ba ta ta’allaka ga kasancewarsa entrepreneur ko employee, kuma ba ta ta’allaka ga mallakar Degree kaɗai ko rashin mallakarsa. Muhimmin abu shi ne mutum ya kasance mai amfani, mai gaskiya, mai ilimi da tarbiyya, kuma ya yi amfani da abin da Allah Ya ba shi wajen kyautata rayuwarsa da ta al’ummarsa.

Allah Ya yi mana zaɓi mafi kyau, Ya ba kowa abin da ya fi dacewa da shi, Ya kuma sa abin da muka nema ya zama alheri a gare mu.

01/08/2026
01/08/2026

@

03/12/2025

Address

Unguwan Sarkin Dokanlere
Lere

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hassan IBN- Salisu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category