Al Ihsan Multimedia

Al Ihsan Multimedia This Is Official page Of Al-Ihsan Multimedia News.

Kotun Abuja ta gurfanar da tsohon Sanata Elisha Abbo kan zargin fyade da ya shafi yarinya ‘yar shekara 13, ta kuma ba sh...
14/01/2026

Kotun Abuja ta gurfanar da tsohon Sanata Elisha Abbo kan zargin fyade da ya shafi yarinya ‘yar shekara 13, ta kuma ba shi beli na Naira miliyan 50.

AFCON 2025: Tinubu ya yaba wa Super Eagles bayan sun doke AlgeriaShugaba Tinubu ya yaba wa kungiyar Super Eagles ta AFCO...
10/01/2026

AFCON 2025: Tinubu ya yaba wa Super Eagles bayan sun doke Algeria
Shugaba Tinubu ya yaba wa kungiyar Super Eagles ta AFCON 2025 bisa gagarumar nasarar da s**a samu da ci 2–0 a kan Algeria, wanda ya ba su damar tsallakewa zuwa wasan kusa da na ƙarshe (semi-finals) na gasar.

Jagoran jam'iyyar APC a jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dawo gida Najeriya daga Dubai, bayan kammala hutunsa ...
10/01/2026

Jagoran jam'iyyar APC a jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dawo gida Najeriya daga Dubai, bayan kammala hutunsa na karshen shekara.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen karbar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a jam'iyyar APC.

Bayan dawowarsa, ana ran Ganduje zai fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Kano, dangane da abubuwan da suke faruwa a jihar.

Da Dumi-Dumi Peter Obi ya koma jam'iyyar ADCDan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour Party a zaben 2023 a Nijeriya,...
31/12/2025

Da Dumi-Dumi

Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour Party a zaben 2023 a Nijeriya, Peter Obi, tare da wasu manyan shugabannin siyasa daga yankin Kudu maso Gabashin kasar, sun bayyana a hukumance cewa sun koma Jam’iyyar ADC.

Shugabannin sun yi wannan sanarwa ne a Enugu, inda s**a taru domin bayyana matsayarsu a bainar jama’a.

Ma’aikacin hukumar NASENI a Najeriya ya zargi Mataimakin Shugaban Hukumar, Khalil Sulaiman Halilu, da hana masa albashin...
11/12/2025

Ma’aikacin hukumar NASENI a Najeriya ya zargi Mataimakin Shugaban Hukumar, Khalil Sulaiman Halilu, da hana masa albashin watanni bakwai tare da tilasta shi ya sa hannu kan wata takarda mai dauke da abin zargi.

Gwamnan jahar Rivers Simunilayi Fubara yakoma jam'iyar APC.Fubara, ya sanar da sauya sheƙar ne yayin wani taron masu ruw...
09/12/2025

Gwamnan jahar Rivers Simunilayi Fubara yakoma jam'iyar APC.

Fubara, ya sanar da sauya sheƙar ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke birnin fatakwal na jihar Rivers.

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da ƴan majalisar jihar 15 tare da kakakin majalisar s**a sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ta APC

Hedikwatar Rundunan Soja Ta Ƙasa Ta Musanta Zargin Kashe Mata Biyu A Lamurde.Hedikwatar Brigade ta 23 ta Rundunar Sojin ...
09/12/2025

Hedikwatar Rundunan Soja Ta Ƙasa Ta Musanta Zargin Kashe Mata Biyu A Lamurde.

Hedikwatar Brigade ta 23 ta Rundunar Sojin Najeriya ta sami labarin wani rahoto marar tushe da Sahara Reporters da wasu kafafen yada labarai na intanet s**a wallafa a ranar Litinin 8 ga Disamba, 2025. Wannan rahoto ya zargi Brigade ɗin da kuma Kwamandanta da tuhumar karya marar tushe.

Akasin wannan zargi, Hedikwatar 23 Brigade na sanar da cewa rahoton ba shi da wata ƙwaƙƙƙar hujja, don haka ya zama rikitacce kuma ya saɓa wa gaskiya. Wannan rahoto ba komai ba ne face yunƙurin bata sunan Brigade da Kwamandanta, tare da gurbata sunan Rundunar Sojin Najeriya baki ɗaya.

Ya zama dole mu sanar da jama’a cewa ba Kwamandan Brigade ba, ko kuma yar dakansa ne s**a kasance a wurin rikicin al’umma, domin a lokacin da ake zargin harbin, Kwamandan Brigade na cikin taron bayanin aikin mako-mako ta yanar gizo tare da Babban Hafsan Sojojin Kasa.

Hedikwatar 23 Brigade tana son fayyace cewa haɗaɗɗun dakarun 23 Brigade Garrison, Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya, NSCDC da DSS sun samu bayanin bullar rikicin al’umma tsakanin kabilun Bachama da Chobo na ƙaramar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa a kimanin ƙarfe 01:35 na safiyar Litinin, 8 ga Disamba 2025.

Rikicin al’ummar ya samo asali ne daga rikicin fili da rashin jituwar kabilanci tsakanin Chobo da Bachama. Dakaru s**a gaggauta isa yankunan da abin ya shafa don dawo da zaman lafiya a kauyukan Tingno, Rigange, Tito, Waduku da Lamurde.

A yayin aikin dawo da doka da oda, wata kungiya ta ‘yan tawayen makiyaya da ake zargin suna goyon bayan daya daga cikin ɓangarorin rikicin—Chobo—ta kai wa dakarun hari. Dakarun, wadanda ƙwararru ne, masu iya sauya dabaru kuma a shirye suke don yaƙi, s**a fatattaki ‘yan tawayen cikin fafatawa. A lokacin musayar wuta, dakarun sun kawar da uku daga cikin ‘yan bindigar, sauran kuma s**a gudu daga yankin. Dakarun sun samu nasarar dakile tashin hankalin.

Daga bisani, dakarun tare da sauran jami’an tsaro sun bi hanyar da ‘yan tawayen s**a gudu ta, inda s**a gano karin gawarwakin mutane biyar da aka kashe tare da babur. Sannan dakarun s**a samu kiran gaggawa cewa wani bangare na al’umma ya shirya kai hari hedikwatar ƙaramar hukumar Lamurde.

A yayin da dakarun ke kan hanyar kare hedikwatar, wasu mata s**a toshe hanya don hana su wucewa, yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin yan asalin Bachama ne s**a yi harbi barkatai a cikin al’umma. Dakaru s**a samu hanyar wucewa s**a ci gaba zuwa hedikwatar don kare wurin. A wannan lokaci, ba a harbi wata mace ba, kuma babu wata da ta ji rauni. Da hakan ta faru, babu yadda dakarun za su samu damar tsallakewa cikin taron jama’ar.

Dakarun sun kare hedikwatar daga maharan. Yayin da suke ajiye a masaukin gwamnati (LGL), aka kawo gawarwakin mata biyu ga wurin, sannan jama’a s**a yi zargin cewa dakaru ne s**a kashe su.

Ba tare da wata shakka ba, mutuwar ta faru ne sakamakon rashin kwarewar da ‘yan tawayen ƙananan al’umma ke da shi wajen sarrafa bindigogi na atomatik.

Duk da haka, Brigade na mika ta’aziyya ga iyalan matan da s**a rasu, tare da kira ga al’ummomin da ke rikici da su rungumi zaman lafiya don kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.

Brigade ta kasance a shirye wajen cika aikinta na kundin tsarin mulki domin tallafawa hukumomin farar hula, kuma za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin kiyaye doka don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da take da alhakin kula da shi.

Hedikwatar 23 Brigade na rokon jama’a da su yi watsi da wannan rahoto na boge.

CPT. OLUSEGUN ABIDOYE
Mai Magana Da Yawun Birged Na 23

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da sunan tsohon Babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa  ga Majalisar D...
02/12/2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da sunan tsohon Babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa ga Majalisar Dattawan Najeriya don amincewa da naɗin sa a matsayin ministan tsaron ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan da Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙamin ministan tsaron.

Gwamnatin Tinubu ta ce ba za ta taɓa yafewa Peter Obi ba saboda goyon bayan da ya ba wa matakin Trump na yunkurin nuna k...
25/11/2025

Gwamnatin Tinubu ta ce ba za ta taɓa yafewa Peter Obi ba saboda goyon bayan da ya ba wa matakin Trump na yunkurin nuna karfin soja akan Najeriya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 Atiku Abubakar ya karɓi...
24/11/2025

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 Atiku Abubakar ya karɓi katin zama ɗan jam'iyyar hamayya ta ADC.

Atiku ya karɓi katin ne a mazaɓarsa a ƙaramar hukumar Jada da ke Jihar Adamawa, mutane da dama s**a taru a wajen karɓar katin.

Mutane da dama na ganin shigarsa ADC a matsayin abin da zai kara wa jam'iyyar tagomashi.

Facebook ta goge asusun Rev. Ezekiel Dachomo bayan wallafe-wallafensa kan zargin kisan kiyashi na Kiristoci a Najeriya.
23/11/2025

Facebook ta goge asusun Rev. Ezekiel Dachomo bayan wallafe-wallafensa kan zargin kisan kiyashi na Kiristoci a Najeriya.

Address

Mubi North LGA
Mubi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al Ihsan Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category