18/05/2026
A yau na samu nasarar gudanar da tantancewa (screening) a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Shira District. Wannan wani babban mataki ne a tafiyarmu ta siyasa da kuma burinmu na kawo cigaba mai ma’ana ga al’ummarmu.
Ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan masu goyon baya, abokai, matasa, da masu fatan alheri da s**a tsaya tsayin daka tare da mu ta hanyar addu’o’i, shawarwari, da ƙarfafawa. Goyon bayan ku na bani ƙarin ƙarfin guiwa da jajircewa.
Wannan tafiya ba tawa kaɗai ba ce, tafiya ce ta al’ummar Shira District baki ɗaya domin ganin an samu shugabanci na gaskiya, cigaba, wakilci nagari, da baiwa matasa dama.
Ina ƙara roƙon ci gaba da addu’o’inku da goyon bayanku yayin da muke ci gaba da wannan tafiya mai muhimmanci. Da yardar Allah, nasara tamu ce.
Shira District sai mun ɗaga ta sama.
Hon. Yusuf Ali Yana
17/05/2027.