20/05/2026
بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا"
Cikin alhini da juyayi muke miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga Limamin Zamaninmu Sahibul Asr (Ajjalallahu Farajahu Sharif), da kuma Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Bisa rasuwar: Marhum Haruna Alhasan Malammadori
Marhum ya rasu ne ranar 18/05 /2026, sakamakon haɗarin mota da ya rutsa dashi a hanyar sa ta dawowa daga wajen neman halas ɗin sa.
Marhum ya kasance matashi kuma mai ƙoƙari da himma wajen ayyukan addini wanda ya bayar da gudunmawa gwargwadon ikon sa.
Haka kuma ya kasance ɗaya daga cikin matasan rundunar Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky ƙarƙashin John Ibn Huwaid Zone.
Muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyayensa, ƴan uwansa da abokansa. Allah ya jiƙansa da rahama, Allah ya karɓe shi a matsayin Shahidi.
Muna roƙon ƴan uwa da su saka Marhum cikin addu’o’insu tare da karanta Suratul Fatiha da Salatin Annabi goma sadaukarwa zuwa ga ruhinsa.
KULLUNA AHMAD YA ABA AHMAD
JASAZ SHUHADA